Ana zargin magidanta biyu da yi wa ’ya’yansu ciki
’Yan banga a garin Suleja Jihar Neja sun kama wasu magidanta biyu bisa zargin yi wa ’ya’yansu ciki. Xaya daga cikin waxanda ake zargin mai suna Kayode da ke zaune a Kwamba a garin Suleja kuma yake harkar xabi’i, ’yarsa ce ta shigar da kara a oifishin ’yan banga kamar yadda Sakatarensu Malam Sulaiman Badaru […]
’Yan banga a garin Suleja Jihar Neja sun kama wasu magidanta biyu bisa zargin yi wa ’ya’yansu ciki. Xaya daga cikin waxanda ake zargin mai suna Kayode da ke zaune a Kwamba a garin Suleja kuma yake harkar xabi’i, ’yarsa ce ta shigar da kara a oifishin ’yan banga kamar yadda Sakatarensu Malam Sulaiman Badaru ya shaida wa Aminiya.
Malam Sulaiman Badaru ya ce da farko yarinyar ta tuntubi wata mata ce da ke tallar maganin gargajiya ta bukaci yin kasuwanci a karkashinta don kula da kanta da xnta mai wata biyu, kamar yadda matar ta bayyana musu. Ya ce matar ta tambaye ta ina iyayenta ko mahaifin xan suke, “A nan ne ta ce ai mahaifinta ne ya yi mata ciki, kuma tuni ya fara matsa mata yana neman ci gaba da lalata da ita bayan haihuwarta, kuma hakan ya sa ta gudu daga gida.
Badaru ya ce, bayan jin bayanin yarinyar ne ya sa aka bi ta zuwa gidansu inda take tare da kanenta. Ya ce bincekensu ya gano cewa mahaifinsu ba ya tare da mahaifiyarsu, kuma ya xauko su ne daga kauyensu inda suke tare da kakarsu zuwa gidansa. Ya ce kanen yarinyar ne ya kai su inda mahaifinsu ke aikin xabi’i aka taso keyarsa, daga bisani aka mika shi ga ofishin ’yan sanda na “A” Dibision da ke Suleja.
Mutum na biyu mai suna Muhammadu Bonbita ana tuhumarsa ne da yi wa agolarsa ciki sau uku yana sa ana zubar da shi. Wanda ake zargin wanda jigo ne a kungiyar masu acabaa kauyen Chaza da ke Suleja, Aminiya ta gano zargin ya biyo bayan tsinkewar jini ne ga yarinyar a yayin zubar da cikin na bayan nan.
Uban goyonta ne ya zargi wani saurayinta tare da kai kararsa ga Dagacin kauyen. Wakilinmu wanda ya ziyarci kauyen, ya ce Dagacin ya gayyaci yarinyar wadda marainiya ce da ke tare da mahaifiyarta da ke auren wanda ake zargin. “Bayan uban goyon ya sake nanata zarginsa a kan saurayin kan yi wa agolar ciki, na nemi jin ta bakin yarinyar, a nan ne ta ce mijin mahaifiyarta ne ya yi mata cikin ba saurayin ba. Kuma ta ce wannan ciki shi ne karo na uku da yake yi mata yana ba ta maganin zubarwa,” inji Dagacin.
Ya ce yarinyar ta ce ta zubar da ciki sau biyu a baya ba tare da matsala ba, sai a na uku ne jini ya xauki lokaci yana zuba, kuma hakan ya xago da wannan bankaxa da takaddama.
An mika wanda ake zargin ga ofishin ’yan sanda na “B” Dibision da ke Suleja, bayan kubutar da shi daga yunkurin auka masa da jama’ar da suka yi dafifi a fadar Dagacin suka yi.
Da Aminiya ta tuntubi sabon Kwamandan ’Yan sandan Suleja, ACP Mathias Asogwa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun mika wanda ake tuhuma na farko ga sashin binciken manyan laifuffuka (CID) da ke Minna, a yayin da mutum na biyu aka gurfanar da shi a gaban wata kotu a garin.