Ana zargin mai fasakwaurin motoci da kashe jami’in Kwastam a Kebbi

Ya kashe jami’in ne a kokarinsa na tserewa, in ji hukumar ta Kwastam

Ana zargin mai fasakwaurin motoci da kashe jami’in Kwastam a Kebbi

Jami’an Kwastam a bakin aiki

An kama wani mutum da ake zargi da kashe wani jami’in Hukumar Kwastam ta Kasa lokacin da yake kan aiki, a kokarinsa na yin fasakwaurin wata mota kirar Toyata Corolla.

Ana dai zargin Abdulwasiu Salawudeen ne da kisan jami’in mai suna Aminu Abdullahi a Karamar Hukumar Yawuri ta Jihar ta Kebbi.

Babban Jami’in hukumar a Jihar, Ben Oramalugo,ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar Alhamis, 13 ga watan Yulin 2023, wajen misalin karfe 4:00 na yamma.

“An kama motar ce kirar Toyota Corolla 2015 mai lambar inji 2TBURHE3FC456204, wacce aka yi ittifakin wani mai fasakwauri ne ya tuka ta, inda ya take jami’inmu a kan titin Tarmac Road da ke Yawuri.

“An garzaya da jami’in zuwa Babban Asibitin gari Yawuri domin samun kulawar gaggawa, amma bayan ba shi taimakon farko, sai aka mayar da shi asibitin kashi da ke Wamakko a Jihar Sakkwato.

“Sai dai abin takaici, ya kwanta dama lokacin da ake kokarin kula da shi. Amma Alhamdulillah, mun sami nasarar kama wanda ake zargin mai suna Abdulwasiu Salawudeen, wanda ke tuka motar, kuma tuni mun kawo shi hekdwatar hukumarmu da ke Birnin Kebbi domin zurfafa bincike.

’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo

Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano

Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad

Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC