Ana zargin mai shekaru 55 da yi wa karamar yarinya fyade a Gombe

An cafke mutumin ne tare da wani matashi mai shekara 18 kan zargin makamanciyar wannan aika-aikar.

Ana zargin mai shekaru 55 da yi wa karamar yarinya fyade a Gombe

Kakakin ‘Yan sandan Gombe, ASP Mahid Abubakar

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta cafke wani mai shekaru 55 kan zargin yi wa wata karamar yarinya mai shekaru 11 fyade ta dubura.

An kuma cafke mutumin ne tare da wani matashi mai shekara 18 kan zargin makamanciyar wannan aika-aikar.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya fitar a wannan Litinin din.

ASP Mahid ya ce “Kwamishinan ’yan sanda mai kula da sashin aikata manyan laifuka CID Hayatu Usman, ya ce a ranar 22 ga watan Oktoban shekarar 2023, wata mai suna Sadiya Wada da ke garin Malam Sidi a Karamar hukumar Kwami ta kai rahoto ofishin ’yan sanda.

“Ta bayyana cewa suna zargin wani mai shekara 55 bisa zargin zakke wa wata yarinya ’yar shekara 11 ta dubura.

Ya ce Sadiya ta bayyana wa ’yan sandan cewa suna zargin mutumin ya yaudari yarinyar ce zuwa bayan wani Asibitin Haihuwa da ke garin na Malam Sidi, inda ya zakke mata ta dubura ba tare da amincewarta ba.

ASP Mahid Mu’azu ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin kuma da zarar sun kammala za su tura shi zuwa kotu.

Ya kuma kara da cewa, har ila yau ’yan sandan sun sake kama wani matashi mai shekara 18 da ke kauye Wili a yankin Karamar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe bisa zargin aikata fyade.

Sanarwar ’yan sandan ta yi nuni da cewa wani mai suna Danjuma Jauro ne ya kai rahoto ofishin ’yan sanda cewa wanda suke zargin yana raka ’yarsa ce zuwa gida da misalin karfe 7:30 na dare, sai ya yi amfani da wannan damar ya zakke mata ta dubura a wani kango da ba a kammala ba.

A cewarsa, wanda ake zargin da yarinyar duk an kai su asibiti domin yi musu gwajin tabbatar da lafiyarsu.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina