Ana zargin makiyaya da kashe mutum 20 a Jihar Adamawa
Akalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wadansu da ake zargi makiyaya ne suka kai hari a kauyen Kudomon da ke karamar Hukumar Demsa a Jihar Adamawa.Wani da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, “An kai mana hari kauyenmu tun ranar Juma’ar da ta gabata, kuma makiyayan sun kone mana kauyen […]
Akalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wadansu da ake zargi makiyaya ne suka kai hari a kauyen Kudomon da ke karamar Hukumar Demsa a Jihar Adamawa.
Wani da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, “An kai mana hari kauyenmu tun ranar Juma’ar da ta gabata, kuma makiyayan sun kone mana kauyen gaba daya. A ranar Juma’ar mutum takwas aka sare wa kai sannan a ranar Asabar da Lahadi makiyayan sun kama mutane suka kuma kashe su a lokacin da suka je daukar gawakin ’yan uwansu da aka kashe.”
Ya ce, “A safiyar yau (Litinin) da mutane suka je binne gawar wata tsohuwa, makiyayan sun sake kai mana hari a makabarta. Kuma da muka ruga zuwa gida sai muka gano cewa sun riga sun zagaye kauyenmu kuma gidajen kauyen gaba daya an kone su sai na tsirarun ’yan uwansu Fulani ne ba su kona ba.”
Ya fadi cikin kuka cewa: “Duk dangina da mutanen da muke takara da su a harkar siyasa an harbe su harbin da gawarwakinsu ma ba za a iya daukowa a binne ba. A yanzu da nake muku magana akwai gawarwaki da dama wadanda ba a binne ba saboda tsoro kada a je garin dauko su a sake kashe mutane. Akwai wadansu gawarwakin da aka kai asibiti wadanda harsasai suka yi musu lahani.
Ya sake fashewa da kuka”
Ya ce bayan haka ne sojoji suka isa da motoci akalla goma da jirgi mai saukar ungulu daya bayan sun gama zagaya cikin kauyen sai suka baro kauyen da misalin karfe 3:00 na yamma.
Ya ce ganin yadda sojojin suka tafi ba su kwana ba, hakan ya sanya tsoro a zukatan mutanen kauyukan da ke makwabtaka da Kodumon kamar kauyen Murgarand da Kulliro da kuma Kudiri.
“kauyukan da ke makwabtaka da kauyen Kodumin sun yi hijira zuwa Demsa saboda tsoron kada makiyayan su kai musu hari,” inji shi.
Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta dauki alkawarin kai ziyara kauyukan domin ganin irin barnar da makiyayan suka yi. Wakilan majalisar daga Demsa da Lamurde sun hada kai da sauran ’yan majalisar don kai taimako kauyukan.
Aminiya ta yi iya kokarin jin tab akin hedkwatar ’yan sandan jihar kan lamarin amma abin ya gagara.