Ana zargin malama da yi wa dalibinta dukan da ya yi ajalinsa a Kano
Sai kawai kawo min shi aka yi ranga-ranga wai ba shi da lafiya.
DSP Haruna Abdullahi Kiyawa
Rundunar ’yan sandan Kano ta kame wata malamar makaranta da ake zargi da yi wa dalibinta dukan da ya yi ajalinsa.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, tuni aka rufe makarantar ta El-Salam Success Academy da ke Unguwar Kurna a Karamar Hukumar Fagge ta Jihar.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Mun gayyato malamar da shugabannin makarantar da ’yan uwan yaron da tuni aka yi wa jana’iza.
Kwamishinan ’yan sanda ya ba da umarnin a mayar da korafin sashen binciken manyan laifuka da ke Shalkwatarmu ta Bompai, bangren kisan kai.
“Yanzu haka ana ci gaba da fadada bincike,” inji Kiyawa.
Iyayen yaron mai suna Surajo Surajo Isa, sun yi zargin cewa malamar ce ta yi sanadiyar mutuwar dansu domin kuwa lafiya kalau ya tafi makaranta a ranar Talata.
Mahaifaiyar yaron dan shekara tara mai suna Hajiya Salma ta ce, “sai kawai kawo min shi aka yi ranga-ranga wai ba shi da lafiya, inda nan take muka garzaya da shi zuwa asibiti.
“Bayan na kai shi asibiti sai likita ya ki taba shi, ya ce wannan yaron me aka yi masa, sai na ce malamarsa ce ta ce baya jin dadi shi ya sa na kawo shi a duba shi.
“Sai likitan ya ce a’a wallahi, wannan akwai abun da ya faru da shi don ga shi wani abu yana bulbula ta hancinsa, ga jini ga kumfa.
“Haka na hakura na koma makarantar na same ta amma ta rika cewa ita ba za ta bi nib a don ba ta san me ya same shi ba.
“Sai wasu ’yan uwanta malamai biyu suke wurin suka rika kakkare wai ba abin da ya samu Surajo.
“Na fashe da kuka na fit azan koma asibitin shi ne suka biyo ni muka tafi tare, kafin mu karasa Allah Ya karbi rayuwarsa,” a cewar mahaifiyar yaron.
Mahaifiyar ta ce tun a baya dan nata yana yawan kai mata korafin cewa malamar tana dukansa, amma sai ta fita batunsa don a ganinta korafi ne na rashin son zuwa makaranta.