Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan mangwaro a makaranta

Mahaifin ɗalibin ya je biyan kudin makarantar inda ya samu malamin yana duka tare da naushin yaron saboda yana shan mangwaro

Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan mangwaro a makaranta

Bulala

Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar.

Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya.

Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa.

Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa.

Ganin halin da ya iske ɗan nasa a sai ya sanya baki, amma malamin bai dakata ba da naushin yaron.

Mahaifin mai suna Bashiru Haman, ya ce, “Na kaɗu da ganin ana dukan yaron haka, na yi ƙoƙarin in ƙwace shi amma malamin ya ƙi barin sa. Daga nan sai an kai ƙara wajen shugabar makarantar, Misis Amanda Pam, Amma sai ta umarce ni da in fice daga harabar makarantar.”

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Adamawa, A’isha Yanar ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce, “ma’aikatar ta samu wasikar ƙorafin mahaifin ɗalibin kuma ta fara gudanar da bincike domin daukar matakin da ya dace. Za kuma mu ɗauki matakan da suka kamata domin hana faruwar irin haka a nan gaba.”

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta ce ta fara gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda kakakinta, Dankombo Morris, ya sanar.

Ya ce, “muna kira da duk masu wani bayani game da abinda ya faru da su taimaka mana da bayanai a wannan bincike da muke gudanarwa.”

A halin yanzu dai yaron mai suna Jaafar yana fama da jinya a yayin da iyayensa suke neman a ƙwato masa haƙƙi kan azabtarwar da aka yi masa.

Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —Babangida

Yadda aka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga

Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan mangwaro a makaranta

NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri