Ana zargin manajan otel da kisan sufeton ’yan sanda
Yan sanda sun kama Manajan Daraktan otel din Pinnacle Guest Inn and Resort Hotels, tare da wasu ma’aikatansa biyar, bisa zarginsu da kashe wani sufeton ’yan sanda ta hanyar yi masa duka.Otel din Pinnacle Guest Inn and Resort Ltd, yana kan hanyar Dange Shuni ta hanyar zagaye ta Gabas a unguwar Tamaje, da ke birnin […]
Yan sanda sun kama Manajan Daraktan otel din Pinnacle Guest Inn and Resort Hotels, tare da wasu ma’aikatansa biyar, bisa zarginsu da kashe wani sufeton ’yan sanda ta hanyar yi masa duka.
Otel din Pinnacle Guest Inn and Resort Ltd, yana kan hanyar Dange Shuni ta hanyar zagaye ta Gabas a unguwar Tamaje, da ke birnin Sakkwato, kuma wuri ne da ya yi suna wajen hada-hada da daddare a Sakkwato.
dan sandan mai suna Sufeto Nura Hashimu dan tsohon Kwamishinan ’Yan sanda Hashimu Yawuri ne, kuma yana aiki ne a Jihar Abiya, inda aka ce ya zauna a otel din na kwana biyar kafin rasuwarsa a ranar Asabar da ta gabata.
Aminiya ta samu labarin cewa an zargi Nura Hashim da aikata abubuwa da ba su dace ba ga ma’aikatan otel din mata, inda ya bugi daya daga cikinsu, lamarin da ya sa Manajan Daraktan otel din ya yi masa magana cewa ya bi dokar wurinsu ko ya tattara kayansa ya kara gaba, amma ba za su amince ya rika wulakanta ma’aikatansu a lokacin da suke yin aiki a dakin da yake zaune ba.
Majiyarmu ta ce wadannan kalamai ne suka harzuka Nura ya mari Manajan Daraktan dan kabilar Ibo, daga nan wasu ma’aikatan da ke tare da shi suka far wa Nura da duka har ya fadi kasa, kuma ana cikin haka ne ’yan sanda suka shigo wurin suka dauke shi zuwa Asibitin kwararru na Jihar inda a can aka tabbatar ya rasu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Al-Mustafa Sani ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce “Mutanenmu da ke kula da Unguwar Tamaje ne da misalin karfe 2:00 dare suka samu labarin akwai matsala a otel din Pinnacle, kuma a lokacin da suka je wurin sai suka samu Nura a kwance bai san in da yake ba, suka dauke shi zuwa Asibitin kwararru inda a can ne ya rasu, yanzu haka ana kan bincike da zarar an kammala za a mika su kotu.”