Ana zargin mata da kashe dan mijinta
Kotun Majistare Mai lamba 57 da ke Nomanslan a birnin Kano ta bayar da umarnin a tsare wata mata a kurkuku bisa zarginta da kashe dan mijinta mai kimanin shekara hudu mai suna Usman Shitu. ’Yan sanda sun shaida wa kotun cewa matar mai suna A’isha Alassan Tudun Murtala ta shake wuyan yaron ne a […]

Kotun Majistare Mai lamba 57 da ke Nomanslan a birnin Kano ta bayar da umarnin a tsare wata mata a kurkuku bisa zarginta da kashe dan mijinta mai kimanin shekara hudu mai suna Usman Shitu.
’Yan sanda sun shaida wa kotun cewa matar mai suna A’isha Alassan Tudun Murtala ta shake wuyan yaron ne a daidai lokacin da yake cin abinci
Da yake bayar da shaida mijin wacce ake zargin kuma mahaifin yaron mai suna Abdullahi Shitu ya ce wata yarinya ce daga cikin ’ya’yansa ta gaya masa cewa ya zo ya ga yadda marigayin yake mimmikewa. “Lokacin da na isa sai na same shi a hannunta (wadda ake zargin), ya ma riga ya rasu. Sai na ga lomar tuwo a hannunsa ga kuma wata a bakinsa. Sai na juya na tambaye ta abin da ya faru in da ta gaya min cewa wai haka kawai ta ga ya fadi,” inji shi.
Mahaifiyar yaron ta roki kotu ta bi mata hakkin danta da aka salwantar.
Sai dai wacce ake zargin ta musanta zargin da ake yi mata, wanda ya saba wa sashe na 221 na Pinal Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Haulatu Magaji Kankarofi ta bayar da umarnin tsare matar a gidan kaso zuwa ranar 9 ga watan gobe don ci gaba da shari’ar.
A wani labarin kuma Kotun Majistare Mai lamba 15 da ke Nomaslan ta bayar da umarnin tsare wani mutum a kurkuku bisa zarginsa da kisan wani matashi.
Tun farko ’yan sanda sun shaida wa kotu cewa wani mutum ne mai suna Aminu Bubbugaje ya shigar da kara ofishinsu da ke Kumbotso yana zargin wani makwabcinsu mai suna Isa Sulaiman Bubbugaje da kisan dansa mai suna Shukrana Lawan ta hanyar daba masa wuka a kirji, sakamakon tashin wata hatsaniya a tsakaninsu.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin wanda ya saba da sashe na 221 na Final Kod.
Alkalin kotun Mai shari’a Mutari Garba dandago ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin har zuwa ranar 8 ga Mayun bana don ci gaba da saurarren karar.