Ana zargin matar aure da karya ’ya’yan kishiya da azabtar da su

’Yan banga a yankin Kwamba da ke Suleja a Jihar Neja suna bincikar wata matar aure mai suna Maryam Idris kan zarginta da musguna wa ’ya’yan kishiyarta dan shekara biyu da yayarsa ’yar shekara hudu inda har ta kai su ga sun samu karaya. Aminiya ta samu labarin cewa mai unguwar yankin da suke ne […]

Ana zargin matar aure da karya ’ya’yan kishiya da azabtar da su
Ana zargin matar aure da karya ’ya’yan kishiya da azabtar da su

’Yan banga a yankin Kwamba da ke Suleja a Jihar Neja suna bincikar wata matar aure mai suna Maryam Idris kan zarginta da musguna wa ’ya’yan kishiyarta dan shekara biyu da yayarsa ’yar shekara hudu inda har ta kai su ga sun samu karaya.
Aminiya ta samu labarin cewa mai unguwar yankin da suke ne ya kai lamarin ga ’yan bangan, bayan ya samu labarin hakan daga makwabta kuma daga nan ne aka gayyato matar da mijinta wanda ke zuwa gidan iyalansa a ranar Lahadin kowane mako sannan ya koma Abuja ranar Litinin inda ya ke sana’ar gasa nama a yankin Zone 4.
A bayanin da ta yi a ofishin ’yan bangan, matar ta zargi yaran biyu da yi mata kashi a cikin dakinsu na kwana da kuma hararwa a duk lokacin da ta ba su abinci a tsawon zamansu na wata biyu bayan mahaifin yaran ya dauko su daga wajen tsohuwar matarsa, al’amarin da ta ce yana takura mata tare da bakanta mata rai musamman ita yarinyar wadda ta ce ta iya magana amma ba za ta sanar da ita za ta yi kashi ba sai dai kawai ta zobo shi a cikin suturar da ke jikinta.
Mahaifin yaran mai suna Malam Abdullahi Muhammad wanda ya ce bai san lamarin da ke faruwa ba sai daga baya, ya ce bayan ya tambayi ’yarsa a kan gocewar kashi da ta samu a hannu, ta shaida masa cewa “Antina ce ta rike hannuna ta tankwara shi da karfi, ya ce daga nan ne aka kai yarinyar wajen mai dori tare da kanenta wanda ya gano cewa kashin kafadarsa ya goce a yayin da yake gyara masa kwanciya,” inji shi.
Mai unguwar yankin Malam Rajab Ibrahim Tafida wanda ya nuna bacin ransa a kan raunuka da yarinyar ta samu a ciki da kuma bayanta sakamakon yawan dukan da ake yi mata, ya ce ya samu bayanin cewa yaran na harar da abincin da take ba su ne a sakamakon tilasta musu na sai sun cinye duk abinci da ta ba su koda sun nuna sun koshi.    Kwamandan ’yan banga na Masarautar Suleja, Malam Musa Muhammad ya ce mahaifin yaran ya amince zai kai yaran wajen mahaifiyarsu da ke Jihar Kano, yayin da wadda ake zargin ta koma dakinta bayan tsare ta a ofishin na wuni guda.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe