Ana zargin matasa biyu da kashe limami a Abuja

Rundunar ’Yan sandan Abuja tana bincike kan kashe Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a a garin Dutse da ke yankin Apo, Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Litinin din makon jiya, bayan azabtar da malamin mai suna Bashir Abubakar wanda dan asalin Unguwar Bakin Kura ne a garin Bauchi da yake karantarwa da limanci a Abuja. […]

Ana zargin matasa biyu da kashe limami a Abuja

Rundunar ’Yan sandan Abuja tana bincike kan kashe Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a a garin Dutse da ke yankin Apo, Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Litinin din makon jiya, bayan azabtar da malamin mai suna Bashir Abubakar wanda dan asalin Unguwar Bakin Kura ne a garin Bauchi da yake karantarwa da limanci a Abuja.

Sai dai matasa biyu masu suna Imrana da Mansur da ake zargi da kisan sun gudu.

Wani dan uwan malamin mai suna Malam Abdullahi Abubakar da ’yan sanda suka sako bayan tsare shi na tsawon kwana 6 kan lamarin, ya shaida wa Aminiya cewa: “Mahaifin marigayi wana ne, kuma da ya zo garin nan a wajena ya sauka kamar shekara biyar ke nan yanzu. Yana koyarwa a babban masallacin garin nan kuma ya na ba da Sallah a can.” Ya ce “Ranar da abin ya faru da misalin karfe 4 na Asuba wani yaro mai suna Abdullahi ya zo kofar dakina ya tashe ni daga barci ya ce in zo ana dukan dana. Na ce wanne daga ciki, sai ya ce Bashar ne. Nan take na taso, ina isa wajen da abin ke faruwa, sai na gan shi a daure Imrana da Mansur sun sa shi a gaba suna ta dukansa. Na nemi sanin dalili amma ba su tanka mini bi, shi ma na tambaye shi me ya hada su, amma bai ce komai ba. To a nan na bukaci su kwance shi, kuma na bukaci ya mike tsaye, bayan ya mike na tambaye shi ko akwai inda yake yi masa ciwo, sai ya ce babu. Sai na ce mu tafi gida. Isarmu gida na debo masa ruwa don ya wanke jikinsa saboda sun bata masa jiki da laka.”

“Na ce ya je ya kwanta zuwa wayewar gari, amma sai ya ce zai tafi masallaci, na hada shi da dana Abdul na ce ya raka shi  masallacin. Abdul na wajen ya yi alwala ya shiga cikin masallaci kafin ya dawo, kamar yadda ya shaida mini. To bayan Sallar ce sai ya dauki babur dinsa da littatafansa ya nufi Unguwar CBN Kuarters inda yake karantarwa. An ce a kan hanyar zuwa ne ya fadi. Na tafi wajen na  iske an riga an kai shi wani karamin asibitin unguwar yana aman jini. To sai ma’aikatan asibitin suka bukaci a kai shi wani babban asibiti a Abuja,” inji Malam Abdullahi.

Wani abokin koyarwar malamin mai suna Malam Ibrahim Sani ya ce yana tare da shi har zuwa karfe 10 na daren da matasalar ta faru, sannan washegari bayan faruwar lamarin ya gaisa da shi a masallaci bayan Sallar Asuba. Ya ce bayan nan marigayin ya nufi Unguwar CBN. Ya ce daga baya ne labari ya zo musu cewa an gan shi a wani waje yashe a kan hanya, inda wani da ke aikin gadin kamfani da ya sanshi ya tallafo shi zuwa masallacinsu tare da taimakon wani a kan Keke NAPEP jini na fitowa ta bakinsa da hanci duk lokacin da ya yi yunkuri.

“Da farko mun kai shi karamin asibitin garin nan, sai  wani a cikin gari kafin mu wuce da shi zuwa Asibitin Kasa na Abuja. A can ne bayan an dauki hoton kansa aka gano cewa wata jijiya ce ta tsinke a cikin kan kuma jini ya malala zuwa cikin kwakwalwarsa, inda likitocin suka ce za su yi masa aiki a kansa don cire jinin. Duk da cewa asibitin sun fara aikin sun bukaci a samo rahoton ’yan sanda, kuma a lokacin ba mu san abin da ya jawo matsalar ba. Daga baya wani ya shaida mana cewa ai an sanar da dan uwansa Malam Abdullahi cewa ga dan uwansa a kwance, ya ce ya san da maganar,  kuma  lokacin da muka bukaci ya bi mu zuwa babban asibitin ya ce ba zai je ba,” inji shi.

Ya ce “A madadin haka sai ya bukaci a ba shi wayar marigayin wadda marigayin ya mika min ita tun yana cikin hayyacinsa. Sai na dauko wayar na mika masa. A nan ne sai aka je aka sanar da Hakimi kan nema rahoton ’yan sanda. Hakimi ya kalubalanci dan uwan nasa kan gaza sanar da hukuma abin da ya faru alhali yana sane. Nan take Hakimi ya karbi wayar marigayin daga hannun dan uwan nasa. Ya nuna masa abin da ya yi laifi ne. Sai aka shiga neman matasan da ake zargi, amma ina sun riga sun gudu.”

Ibrahim Sani ya ce matasan ’yan asalin Jihar Taraba ne kuma sun gudu ne tare da mai gidansu mai suna Isa da suke sana’ar fawa a karkashinsa, kuma shagonsu na daura ne da na Malam Abdullahi  ne wanda shi ma fawar yake yi.

Wani makusancin marigayin mai suna Malam Mas’udu Aliyu, ya ce a farko zuwan marigayin a gidan dan uwansa yake zaune amma, ya fi kwana a wajen daliban ilimi ’yan uwansa, wani lokaci kuma ya shafe dare a masallaci ko a cikin ajin da ke harabar masallacin yana karatu. Ya ce marigayin wanda hafizin Alkur’ani ne ya samu gurbin karatu zuwa wata kasar waje kafin Karamar Sallah, inda yake zargin hakan yana iya jawo kyashi daga cikin wadanda ake zargi da hannun a lamarin.

Babban Limamin Masallacin Malam Abdulhamid Imam, ya ce lokacin da lamarin ya faru ba ya gari. Ya ce bayan samun labarin ya dawo kuma bayan an yi masa Sallar Jana’iza, shi da wadansu sun je ta’aziyya ga mahaiifiyarsa da ke garin Bauchi.

DPO din yankin Apo, CSP Emega John wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bayan  an kama dan uwan marigayin wato Malam Abdullahi da kuma wani mai suna Kabiru tare da kai su zuwa Sashin Binciken Manyan Laifuffuka (CID) na Rundunar ’Yan sandan Abuja daga bisani aka ba da belinsu.