Ana zargin matasa da kashe dattawa ta hanyar tsafi a Binuwe
Hakimin Tyoshin, Cif Daniel Abomtse, ya zargi matasa da kashe dattawa ta hanyar tsafi a karamar hukumar Gwer-West ta jihar Binuwe. Abomtse ya bayyana haka ne a wajen bikin binne Mai ba Gwamnan Binuwe Shawara kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Jerome Torshimbe. Dan sandan da ya yi kisa zai shekara bakwai a kurkuku Dan sandan da ya […]
Hakimin Tyoshin, Cif Daniel Abomtse, ya zargi matasa da kashe dattawa ta hanyar tsafi a karamar hukumar Gwer-West ta jihar Binuwe.
Abomtse ya bayyana haka ne a wajen bikin binne Mai ba Gwamnan Binuwe Shawara kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Jerome Torshimbe.
- Dan sandan da ya yi kisa zai shekara bakwai a kurkuku
- Dan sandan da ya yi kisa zai shekara bakwai a kurkuku
Abomtse ya ce akalla dattijan talatin sun rasa rayuwakansu sakamakon sihiri da ake yi musu a gargajiyance.
Ya ce, “kisan dauki dai-dai da matasa ke yi wa dattawa ta hanyar amfani da bokaye ya halaka fiye da mutum 30 daga shekarar 2012 zuwa yau.”
“Karamar hukuma ta yi iya kokarin ganin an hana faruwar hakan amma bai yiwu ba saboda haka muke rokon Gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki kan masu kisan da matsafan,” inji shi.
Da yake bayani, Gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya gargadi matasan kan mummunar dabi’ar tare da cewa duk wanda aka kama da laifin zai dandana kudarsa.
Ya kuma ce duk wani matashi da aka kama yana zuwa wajen bokaye domin cutar da wani zai fuskanci fushin gwamnati.