Ana zargin matashi da yi wa matar kawunsa fyade
Kotun Majistare da ke Sakatariyar Audu Bako a Kano ta tsare wani matashi da ake zargi da yi wa matar kawunsa fyade. ’Yar sanda mai gabatar da kara Sufeto Mercy John ta shaida wa kotun cewa matashi mai suna Saifullahi Haruna ya dauko hayar wani mutum da ake kira Sulaiman Auwal wadanda dukansu mazauna garin […]
IGP

Kotun Majistare da ke Sakatariyar Audu Bako a Kano ta tsare wani matashi da ake zargi da yi wa matar kawunsa fyade.
’Yar sanda mai gabatar da kara Sufeto Mercy John ta shaida wa kotun cewa matashi mai suna Saifullahi Haruna ya dauko hayar wani mutum da ake kira Sulaiman Auwal wadanda dukansu mazauna garin Kabo ne inda suka hadu suka yi wa matar kawunsa (wacce aka saya sunanta) fyade.
Tuni dai wadanda ake zargin suka amsa laifinsu na hadin baki da yin fyade laifuffukan da suka saba wa sashe na 97 da 231 na Kundin Shari’a na Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Salma danbaffa ta bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargin a kurkuku har zuwa ranar 10 ga watan Mayu, 2018, domin ci gaba da sauraren shari’ar.
A wani labarin kuma an gurfanar da wadansu jami’an ’yan sandan farin kaya a gaban
Kotun Majistare Mai lamba 17 da ke Nomanslan a birnin Kano, bisa zarginsu da cin zarafin wata budurwa mai suna Marwanatu Hassan saboda bashin da ake bin mahaifinta.
Lauyan budurwar mai suna Barista Aliyu Faruku ya bayyana wa kotu cewa jami’an farin kayan su biyu da suka hada da Alanguburo da Alhaji Lawan da Musubahu sun kama budurwar ta tare da kai ta wani wuri wanda ta ce ba ta ma san ko ina ba ne inda suka ci mutuncinta. “Da suka kai ta wurin sai suka fara zazzaginta tare da fasa mata kai da dutse. Sannan suka cire mata hijabi tare da taba mata kirji. Sannan suka kwace mata wayoyinta guda biyu. Haka kuma daya daga cikinsu ya firgita ta inda har ya rika nuna ta da bakin bindiga,” inji lauyan.
Alkalin kotun Mai shari’a Mutari Garba dandago ya umarci ’yan sanda su fadada bincike a kan lamarin tare da dage shari’ar zuwa ranar 2 ga Mayu, 2018.
Sai dai lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hukumar ’Yan sandan Farin Kaya ASP Ibrahim ya ce zarge-zargen ba su da tushe ballantana makama. “Babu wata kotu da ta rubuto mana takarda cewa mu zo kotu mu yi bayani a kan irin wannan magana. Kuma ma ai Kotun Majistare ba ta da hurumin tuhurmarmu,” inji shi.