Ana zargin matashi da yunkurin kashe mahaifinsa
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi a kurkuku bisa yunkurin kashe mahaifinsa sakamakon yi masa fada. Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Sani Shehu ya yi kara gaban ’yan sandan da ke yaki da daba […]
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi a kurkuku bisa yunkurin kashe mahaifinsa sakamakon yi masa fada.
Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Sani Shehu ya yi kara gaban ’yan sandan da ke yaki da daba a Karamar Hukumar Gwale cewa wani dan uwansa mai suna Isma’il Shehu Isma’il Sharada Ja’en ya fiddo wuka ya yi yunkurin daba wa mahaifinsu mai suna Shehu Isma’il mai kimanin shekara 70 sakamakon haka ya yanki wani dan uwansu mai suna Abdulhadi har ma ya kai ga raunata shi a bayansa.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi na yunkurin kisan kai da kuma jawo rauni, laifuffukan da suka saba da sashe na 95 da 246 na Kundin Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Sani Sarki Yola ya bayar da umarnin tsare matashin a kurkuku tare da dage shari’ar zuwa ranar 2/4/2020.