Ana zargin mutum biyu da kashe direban Keke Napep a Borno

An gano gawar direban Napep din bayan kwanaki biyu da kashe shi.

Ana zargin mutum biyu da kashe direban Keke Napep a Borno

Ana zargin wasu mutum biyu da laifin kashe wani direban babu mai kafa uku da aka fi sani da Keke Napep a Jihar Borno.

Wata sanarwa da rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta fitar a wannan Larabar ta ce ta samu nasarar cafke ababen zargin biyu.

Sanarwar ta ce rundunar bayan tattara bayanan sirri ta samu nasarar cafke Simon Buba da Anias Dauda jiya Talata a birnin Maiduguri.

Rundunar ’yan sandan ta ce mutum uku ake zargi da wannan aika-aika, inda kawo yanzu ba ta kai ga cafke na ukun ba wanda aka bayyana da suna James.

Bayanai sun ce wadanda ake zargin sun kashe direban babur din mai shekaru 20 sannan suka binne gawarsa.

Sai dai an gano gawar direban Napep din bayan kwanaki biyu da kashe shi, inda kuma aka mika wa iyalansa domin yi masa jana’iza.

Yayin amsa tambayoyi, wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun kashe direban Napep din ne lokacin da ya dauke su a matsayin fasinjoji zuwa unguwar Shagari Low Cost.

“Bayan ya dauke mu sai muka ce ya bi ta hanyar Dubai.

“Muna cikin tafiya sai muka tsayar da shi a hanya, sai James ya yi amfani da wukarsa ya caka masa ita,” inji daya daga ababen zargin da ke hannu.

A cewarsa, aniyarsu ta kwace babur din ne kawai amma James ya buge shi, ya kuma ba da shawarar a binne shi.

“Mun yi kokarin gaggauta sayar da Keke Napep din a washegari a kan Naira miliyan 1.2, amma James ya dage cewa sai Naira miliyan 1.3, haka muka hakura ba a siyar ba.

“Bayan kwana daya sai aka sake kiranmu mu kawo keken da cewa za a siya kan Naira miliyan 1.3, amma sai aka yi rashin sa’a James ba ya kusa.

“Amma sai muka sha jinin jikinmu cewa tarko ne aka dana mana, domin ‘yan sanda sun kama mu,” in ji Simon.