Ana zargin shugaban karamar hukuma da kisan kai a Jigawa
Ana zargin shugaban karamar Hukumar Jahun da ke Jihar Jigawa, Alhaji Idris danlawan da magoya bayansa da kashe wani mai goyon bayan Jam’iyyar APC mai suna Malam Ya’u Husaini Magama a kauyen Magama da ke karamar hukumar.Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne lokacin da marigayi Ya’u ya jagoranci wasu matasa suka rika cewa […]
Ana zargin shugaban karamar Hukumar Jahun da ke Jihar Jigawa, Alhaji Idris danlawan da magoya bayansa da kashe wani mai goyon bayan Jam’iyyar APC mai suna Malam Ya’u Husaini Magama a kauyen Magama da ke karamar hukumar.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne lokacin da marigayi Ya’u ya jagoranci wasu matasa suka rika cewa “Ba ma yi” lokacin da shugaban ya jagorancin kamfe dinsa zuwa kauyen.
Wani da lamarin ya auku a kan idonsa mai suna Bala Magaji ya shaida wa wakilinmu cewa ya ce suna tare da marigayin lokacin da lamarin ya faru. “Ya’u yana tare da mu a filin taron kauyen, lokacin da Shugaban karamar Hukumar Jahun din ya iso da magoya bayansa daga Kanwar Masabar. Kuma Ya’u na ganin ayarin shugaban ya ce, “Ba ma yi,” sai shugaban ya tsayar da motarsa ya fito ya tambaye mu way a fadi haka, sai Ya’u ya a,sa cewa, “ba wanda yake tare da kai.” Sai shugaban ya shake wuyar rigar marigayin yayin da ’yan bangar siyasa suka hau dukansa. Ya’u ya fadi a kasa, kuma kafin mu kais hi asibiti rasu. ’Yan bangar siyasa sun auka wa shugaban da kanensa Aminu, amma ba su yi musu rauni masu muni ba. Sun taba yi mana haka a shekarar 2011; don haka muna son gwamnati ta yi wani abu a kai kafin lamarin ya baci,” inji shi.
Wani da lamarin ya auku kan idonda mai suna danjummai Ibrahim ya yi zargin cewa shugaban ya fito da wata adda a hannunsa daga cikin mota, amma bai sani ba ko shugaban ya sari Ya’u da ita. Amma ya ce magoya bayan shugaban sun yi wa marigayin sukuwar Sallah da makamai har sai da ya fadi ya mutu.
A lokacin da wakilimmu ya tuntubi Alhaji Idris danlawan ya tabbatar da cewa ya je yankin don kamfe, amma ya ce bai kai hari ga marigayin ba, kuma bai ba da umarni a kai masa hari ba. Ya ce DPO din ’yan sandan yankin ne ya shaida masa cewa wani ya mutu.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa Mista Theophilus Kayode ya tabbatar da mutuwar matsahin inda ya ce an kai rahoton lamari ga ofishin ’yan sanda da karfe 11:00 na dare inda ’yan sanda suka isa da karfe 2:00 na dare. Ya ce rahotanni sun nuna cewa wani dan Jam’iyyar PDP ne ya kashe wani dan Jam’iyyar APC a kauyen.
Ya’u Husaini mai shekara 30 yana da mace da ’ya’ya uku kuma yana shirin angwancewa a gobe Asabar ne ya hadu da ajalinsa. Tuni ’yan uwan marigayin suka karbi gawarsa daga hannun ’yan sanda inda suka yi mata sutura kamar yadda addininn Musulunci ya tanada.