Ana zargin shugaban sakandare da yin fashin bankin Offa – ‘Yan sanda

Ana zargin shugaban makarantar sakandare Michael Adikwu da aka kashe a fashin bankin da aka yi a garin Offa a jihar Kwara ranar 5 ga watan Afirilu 2018. Hedkwatar ‘Yan sandan jihar ta mika rahoton rasuwar Adikwu zuwa ofishin Kwamishinan Shari’a na jihar Kwara Kamaldeen Ajibade ranar Talata. Ajibade, ya bayyana hakan ne yayin da […]

Ana zargin shugaban sakandare da yin fashin bankin Offa – ‘Yan sanda

Ana zargin shugaban makarantar sakandare Michael Adikwu da aka kashe a fashin bankin da aka yi a garin Offa a jihar Kwara ranar 5 ga watan Afirilu 2018.

Hedkwatar ‘Yan sandan jihar ta mika rahoton rasuwar Adikwu zuwa ofishin Kwamishinan Shari’a na jihar Kwara Kamaldeen Ajibade ranar Talata.

Ajibade, ya bayyana hakan ne yayin da ake zargin wasu mutum biyar da ake zargi da aikata fashin bankin Offa, wanda aka gurfanar da su a gaban babban kotun jihar a yau Laraba.