Ana zargin soja da harbe fasinja a Kuros Riba

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti-Allah ta Kasa reshen Jihar Kuros Riba, Alhaji Ya’u Adamu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta rage yawan shingayen da jami’an tsaro da ke duba motoci a kan hanyoyin da suka fito daga jihohin Kudu zuwa na Arewa saboda yadda jami’an suke gallaza wa direbobi kan karbar nagoro idan […]

Ana zargin soja da harbe fasinja a Kuros Riba

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti-Allah ta Kasa reshen Jihar Kuros Riba, Alhaji Ya’u Adamu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta rage yawan shingayen da jami’an tsaro da ke duba motoci a kan hanyoyin da suka fito daga jihohin Kudu zuwa na Arewa saboda yadda jami’an suke gallaza wa direbobi kan karbar nagoro idan direba ya ki bayar wa yadda suke so, sai su wulakanta shi, wani lokacin ma har da cin zarafi.

Shugaban ya ce, “Na baya-bayan nan shi ne ranar Lahadin makon jiya an yi zargin cewa wani soja da ke aiki a barikin soja da ke garin Ogoja  a  Jihar Kuros Riba ya harbe wani fasinja da ke cikin mota ya mutu, a kan karbar nagoro lamarin da ya jawo takaddama mai tsawo a tsakanin Kungiyar Miyetti-Allah ta jihohin Kuros Riba da Taraba kan kisan.”

Alhaji Ya’u Adamu,  ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “Wani direba ne ya taso daga Lobanta a Jihar Abiya  zuwa Kuros Riba zai wuce ya tafi gida ya dauko wasu  kaya da ba da suka zo wani shingen duba motoci da ke mararrabar Ogoja a Jihar Kuros Riba, sai jami’an tsaro suka duba su, sun wuce kwatsam sai wani soja ya tuko mota ya biyo bayan direban motar ya tsayar da shi ya ce sai ya duba kayan da ya dauko. Nan take sojan ya fara harbi a iska ya dawo ya harbi marufin kofar motar ashe akwai wani fasinja ciki kwance da bai san abin da ake yi ba sai harsashi ya bi ta ciki ya same shi wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwarsa, sunan fasinjan Umar Muhammad.”

Kazalika Shugaban Kungiyar Miyetti-Allah ya ci gaba da cewa, “Domin wutar rikicin ta kwanta sojojin sun bayar da Naira dubu 300 aba iyalan mamacin babu mamaki ya bar yara, shi kuma sojan da ya yi harbin sun kawo sojoji su sun tafi da shi, mu kuma mun gamsu da diyyar da suka bayar har ma an umarci motocin da suka rufe hanya su bude a ci gaba da zirga-zirga kura ta lafa,” inji shi.

A karshe ya nemi Gwamnatin Tarayya ta duba artabun da ake yi tsakanin direbobin motoci da jami’an tsaro da masu duba motoci a kan manyan hanyoyi suna karbar na goro suna harbi har su kai ga kisa don ba a basu kudi ba.

“Akalla muna kashe sama da Naira dubu 400 wajen bayar da na goro, yanzu idan mutum ya saro kaya zai kai kasuwa idan bai rike kudade masu yawa  don ba jami’an tsaro ba wulakanci da duka wani zubi ma har kisa suna yi. Do haka a rage yawan jami’an ko a cire su kwata-kwata daga kan hanya,” inji shi.

Dangane da kisan kai da ake zargin soja da  yi wakilinmu ya tuntubi Kakakin Bataliya ta 13 da ke Kalaba inda ta ce, sun samu rahoto har ma sun tura jami’an su daga Kalaba su je wurin domin tabbatar da gaskiyar lamarin.