Ana zargin su da bata sunan matar aure a intanet

’Yan sanda a Kano sun kama wadansu mutane bisa zarginsu da bata sunan wata matar aure mai suna Bushira Madaki a shafin sada zumunta na Whatsapp, inda suka yada labarin cewa tana satar yara a unguwannin Hotoro da dan Marke a birnin Kano. Aminiya ta jiyo cewa baya ga labarin, wadanda ake zargin da suka […]

Ana zargin su da bata sunan matar aure a intanet
Ana zargin su da bata sunan matar aure a intanet

’Yan sanda a Kano sun kama wadansu mutane bisa zarginsu da bata sunan wata matar aure mai suna Bushira Madaki a shafin sada zumunta na Whatsapp, inda suka yada labarin cewa tana satar yara a unguwannin Hotoro da dan Marke a birnin Kano.

Aminiya ta jiyo cewa baya ga labarin, wadanda ake zargin da suka hada da Ummi Aminu da Binta Tijjani da Ibrahim Hassan sun watsa har da hoton matar wadda suka ce tuni ta fada komar ’yan sanda a Kano.

Duk da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, sai dai sun nuna cewa ba su yi haka don bata mata suna ba, sun yi ne don ceto rayukan yaran jama’a. “Mu gaskiya ba mu san matar ba balantana mu bata mata suna. Abin da ya faru shi ne, an turo mana wannan magana ce tare da rokonmu  cewa idan mun karanta mu watsa a wasu wuraren don taimakon al’umma, inda mu kuma muka aikata hakan ba tare da tunanin labarin gaskiya ne ko karya ba,” inji su.

Yayin da take karin bayani ga manema labarai, Hajiya Bushira Madaki, wacce ma’aikaciyar asibiti ce a Jihar Kano, ta ce “Bayan da wata ’yar uwata ta gaya mini labarin abin da ke faruwa, hankalina ya yi matukar tashi. Hakan ya sa na yi kara gaban ’yan sanda, wadanda suka yi kokarin gano wadanda suka watsa wannan labari, wanda babu ko kanshin gaskiya a ciki. Ba na wannan harka, ban kuma san masu yin ta ba.”

A jawabinsu daban-daban, wadanda ake zargin sun nemi afuwar wadda suka bata wa suna, suka ce sun yi abin ne ba da nufin cutar da ita ba.

Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya ce hukumarsu za ta fadada bincike don gano duk wanda ke da hannu a kan shirya wannan labari marar tushe, don gurfanar da shi a gaban kotu. Ya nemi al’ummar Jihar Kano da sauran duniya gaba daya da su yi watsi da wancan labari, kasancewar babu kanshin gaskiya a ckinsa. “Wannan mata ba a taba kai ta ofishin ’yan sanda da suna laifi ba, don haka muna kira ga al’umma su yi watsi da wannan labari da aka baza tare da yin tofin Allah-tsine ga duk wanda ya shirya al’amarin.”