Ana zargin Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki

kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da ‘yan tawayen kasar da laifukan yaki da na keta hakkin dan Adam, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana shekaranjiya Laraba. A wani bincike da kungiyar ta yi, wanda tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranta, ta bayyana yadda aka gallaza […]

Ana zargin Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki
Ana zargin Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki

kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da ‘yan tawayen kasar da laifukan yaki da na keta hakkin dan Adam, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana shekaranjiya Laraba.

A wani bincike da kungiyar ta yi, wanda tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranta, ta bayyana yadda aka gallaza wa fararen hula, ciki har da yi musu fyade da tilasta musu cin naman mutum.
Sai dai rahoton ya ce babu wata alama da ke nuna cewa an ci zarafin mutanen ne saboda dalilan kabilanci.
Rahoton ya kara da cewa rikicin kasar ya fara ne tsakanin sojojin da ke tsaron shugaban kasar, har ya kai gwamnati ta fara kashe ‘yan kabilar Nuer.
Sai dai rahoton ya musanta cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar, dan kabilar Nuer, ya yi kokarin juyin mulki.