Ana zargin suruki da batar da ’yar yar matarsa
Jami’an tsaro a garin Dakwa da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja sun kama wani magidanci mai suna Jibrin Abubakar bisa zarginsa da hannu a bacewar wata buduruwa mai shekara 17, wacce ’yar uwar matarsa ta biyu ce. Tun farko, mahaifiyar yarinyar ce mai suna Binta Lawan ta shigar da kara kan lamarin, bayan rashin ganin […]
Jami’an tsaro a garin Dakwa da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja sun kama wani magidanci mai suna Jibrin Abubakar bisa zarginsa da hannu a bacewar wata buduruwa mai shekara 17, wacce ’yar uwar matarsa ta biyu ce.
Tun farko, mahaifiyar yarinyar ce mai suna Binta Lawan ta shigar da kara kan lamarin, bayan rashin ganin ’yarta mai suna Lauratu Lawal, kamar yadda ta shaida wa Aminiya.
Jibrin, wanda ake tuhuma shi yake auren daya daga cikin kannen mahaifiyar yarinyar da ta bace, wadda kuma ta girma a gabanta kafin ya aure ta kamar shekara uku da suka gabata.
A zantawa da wakilinmu, mahaifiyar yarinyar ta yi zargin cewa a ranar 1 Junairun nan, wanda ake zargin ya yi wa ’yarta waya lokacin da suke tare a gida, inda ya bukaci ta fito daga layin gidansu zuwa bakin titi a garin Dakwa. Ta ce “Ya sanar da ita cewa ya zo ne ya duba ni da jiki amma yana jin nauyin shigowa shi kadai. Saboda haka yana bukatar ta je ta same shi su karaso tare.”
“A lokacin tana cikin yi mini wankin sutura amma sai na yi mata izini, ta dauki hijabinta ta fita da misalin karfe 2:00 na rana. Sai dai tun daga wancan lokaci, ba ta sake dawowa gida ba,” inji Binta.
Ta ci gaba da cewa “Bayan kamar awa biyu sai na bukaci yayarta ta zo gida a lokacin. Da ta kira lambar wayar Jibrin don jin ina take, amma da aka kira shi a wayar bai dauka ba, sai bayan kamar bugawa 10 ne wani ya amsa wayar tasa amma sai ya ce “Wrong Number.” Wato ba shi ba ne. Da ta sake bugawa ne sai Jibrin ya amsa wayar da kansa. Na tambaye shi ina ’yata take sai ya ce sun dade da rabuwa,’ inji ta.
Ta ce “Washegari ne bayan kanena ya zo na sanar da shi lamarin, sai ya samu nasarar samun wayarta da yamma, inda ta yi korafin cewa Jibrin ya mika ta ga wadansu mutane da suka tsare ta a cikin wani bene da ba ta san inda yankin yake ba.”
Aminiya ta samu labarin cewa ’yan sanda sun kama wanda ake zargin a ranar 4 ga Janairu, kafin daga bisani su ba da belinsa a ranar 9 ga wata, bayan alkawarin zai kawo yarinyar ga ofishin ’yan sanda, kamar yadda Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba CSP Muhammad Yahaya, ya tabbatar.
Babban Jami’in ’Yan sandan wanda ya kuma tabbatar da dawo da lamarin zuwa ofishinsa a ranar Talatar da ta gabata, ya ce wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa na hannau a bacewar yarinyar, inda ya ce ya rabu da ita tun a unguwarsu. Sai dai ya ce ofishin zai mika shi ga Babbar Hedikwatarsu ta Abuja don zurfafa bincike a kan lamarin, kasancewar wanda ake zargin, ya gaza kawo yarinyar a cikin kwana biyar da ya bukaci a ba shi lokacin da ake tsare da shi a karamin ofishinsu da ke garin Dakwa.