Ana zargin tsohon kansila da laifin fyade
Wani tsohon kansila mai suna dantala Ahmad ya gurfana a gaban wata Kotun Majistare da ke Zungeru a Sabon Garin Kano bisa zarginsa da yi wa wata yarinya fyade.dantala Ahmad mai shekara 35 mazaunin Bugan kosawa da ke karamar Hukumar Kura a Jihar Kano ana zarginsa da yi wa yarinyar mai kimanin shekara 15 (an […]
Wani tsohon kansila mai suna dantala Ahmad ya gurfana a gaban wata Kotun Majistare da ke Zungeru a Sabon Garin Kano bisa zarginsa da yi wa wata yarinya fyade.
dantala Ahmad mai shekara 35 mazaunin Bugan kosawa da ke karamar Hukumar Kura a Jihar Kano ana zarginsa da yi wa yarinyar mai kimanin shekara 15 (an sakaye sunanta) fyade.
Takardar karar wadda dan sanda mai gabatar da kara Kofur Sulaiman danladi ya karanta ta bayyana mahaifin yarinyar Malam Abdurrazak ne ya kai kara ofishin ’yan sanda inda ya ce tun a shekarar 2011 wanda ake zargin ya dauki ’yarsa ta rika yawon yakin neman zabe da ita.
Takardar ta ci gaba da cewa a daidai wannan lokaci ne tsohon kansilan ya yaudari yarinyar ya yi mata fyade kuma daga nan ta samu juna biyu ta haifi namiji wanda a yanzu haka ya kai shekara daya da wata tara da haihuwa.
Sai dai da aka waiwayi wanda ake zargin ya musanata laifin da ake zarginsa, wanda mai gabatar da karar Kofur Sulaiman danladi ya ce ya saba wa sashi na 283 na kundin shari’ar Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Fauziyya Isa Sheshe ta ce kotun ba ta da hurumin yin hukunci game da wannan laifi mai girma, don haka ta dage shari’ar zuwa ranar 5 ga Mayu tare da bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan kurkuku.