Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa
Ababen zargin da ke hannu sun alaƙanta abin da suka aikata da sharrin shaiɗan.

Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali.
Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada.
- Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara
- Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine
Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu.
Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta kuma bayyana cewa ababen zargin sun yi iƙirarin aikata laifin da suka alaƙanta da sharrin shaiɗan.
Kwamishinan ’yan sandan jihar CP Dankombo Morris, ya tabbatar da cewa za a yi adalci a lamarin, yayin da yake kira ga al’umma da su kasance masu lura da miƙa rahoton duk wani motsi da su aminta da shi ba zuwa ofishin mahukunta mafi kusa.