Ana zargin wani Dagaci da lalata da wata mace a Jigawa
’Yan sanda a yankin karamar Hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa sun kama Dagacin garin Kachi mai suna Shafi’u Abdullahi Kachi bisa zarginsa da laifin yin lalata da wata mace mai suna Sakina da ke zaune a kauyan Kachi da ke karamar Hukumar Dutse. ’Yan sanda sun damke Dagacin ne a otel din Kiyawa Motel kimanin […]
’Yan sanda a yankin karamar Hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa sun kama Dagacin garin Kachi mai suna Shafi’u Abdullahi Kachi bisa zarginsa da laifin yin lalata da wata mace mai suna Sakina da ke zaune a kauyan Kachi da ke karamar Hukumar Dutse.
’Yan sanda sun damke Dagacin ne a otel din Kiyawa Motel kimanin mako biyu da suka gabata a daidai lokacin da wasu matasa suka ingizo keyarsa daga cikin otel din da ake zargin wuri ne na shakatawar wasu fittatun mutane a jihar.
Bayanai sun nuna cewa matasan suna kokarin yi wa Dagacin tsirara, har sun samu nasarar cire masa sutura daga shi sai gajeren wando sai ’yan sanda suka cece shi daga baya suka ci gaba da bincike a kan lamarin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ASP Abdu Jinjiri wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce gaskiya ne an kama Dagacin bisa zargin aikata lalata da wata mace kuma tuni sun gabatar da shi a gaban kotu domin yi masa hukunci.
’Yan sandan sun gabatar da Dagacin da ake zargi ne a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse.
Dagacin wanda ya dauki lauya ya musanta laifin da ake zargin ya aikata, kuma wadanda suke zargin cewa ya aikata wancan laifi, sun gaza bayyana a gaban kotu inda a sakamakon haka alkalin kotun Mai shari’a Yahaya Ibrahim Yayari ya dage sauraran karar zuwa ranar 20/11/14.
Wani dan uwan Dagacin da ya nemi a sakaye sunansa ya ce ba wani abu ya sa ake wa dan uwansu bi-ta-da kulli ba sai saboda rashin jituwa a tsakaninsa da wasu manya a masarautar Dutse da suke sa wa a ci masa mutunci domin ya hana su yi kama- karya.
Ya ce ba don sarauta gado ba ce da sun hakura da ita saboda irin masifar da suka samu kansu a ciki.