Ana zargin wani maigadi da yin lalata da mata ‘yan firamare 54
Hukumomi a Afrika ta Kudu sun tsare wani mai gadi bisa zarginsa da laifin cin zarafin yara ’yan firamare mata su 54. A ranar Litinin aka soma bincike kan batun, bayan da wasuddalibai mata biyu suka kai kara, kuma tuni gwamnati ta tura jami’ai zuwa makarantar da ke Soweto a kudancin Johannesburg. Yara ’yan mata […]

Hukumomi a Afrika ta Kudu sun tsare wani mai gadi bisa zarginsa da laifin cin zarafin yara ’yan firamare mata su 54.
A ranar Litinin aka soma bincike kan batun, bayan da wasuddalibai mata biyu suka kai kara, kuma tuni gwamnati ta tura jami’ai zuwa makarantar da ke Soweto a kudancin Johannesburg.
Yara ’yan mata biyu ’yan shekaru 8 da kuma 12 ne suka je ofishin ’yan sanda a ranar Litinin, inda suka kai kara cewa wani mai gadi ya yi lalata da su a wata makarantar firamare da ke Soweto.
Tun lokacin da aka soma bincike, sai aka gano cewar mutumin ma ya ci zarafin dalibai mata 52.
Kuma ya shafe wata 18 yana tafka ta’asar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
A ranar Laraba ne ake sa ran mai gadin zai bayyana gaban wata kotun Majistre a Soweto.
A halin yanzu kuma sashen ilimi na yankin ya tura jami’ai domin taimakawa ’yan yaran da aka ci zarafinsu sannan kuma a fadada bincike.
Afirka ta Kudu ta kasance daya daga cikin kasashe da aka fi aikata fyade da kuma cin zarafin mata a duniya.