Ana zargin wasu da kashe dan uwansu bisa zargin maita

Wasu mutane hudu da a ke zarginsu da kashe wani magidanci a kauyen Zangon Gitata da ke karkashin gundumar raya kasa ta Panda a karamar hukumar Karu ta Jihar Nassarawa, na fuskantar bincike a hanun rundunar ’yan sandan  jihar da ke Lafiya, bayan an kama su kwana biyu da faruwar lamarin wanda ya auku a […]

Ana zargin wasu da kashe dan uwansu bisa zargin maita
Ana zargin wasu da kashe dan uwansu bisa zargin maita

Wasu mutane hudu da a ke zarginsu da kashe wani magidanci a kauyen Zangon Gitata da ke karkashin gundumar raya kasa ta Panda a karamar hukumar Karu ta Jihar Nassarawa, na fuskantar bincike a hanun rundunar ’yan sandan  jihar da ke Lafiya, bayan an kama su kwana biyu da faruwar lamarin wanda ya auku a ranar 28 ga watan da ya gabata a wani daji da ke kusa da kauyen. Lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci kauyen da ke kan titin Keffi zuwa Jos a ranar Talata da ta gabata, ya samu labarin cewa wadanda a ke zargin su uku daga cikinsu ’yan uwan marigayin ne, sun kashe shi ne bayan sun jima suna barazanar aikata hakan a sakamakon zargi da suke yi masa na maita.
Marigayin wanda malamin makaranta ne, mai duba ayyukan Malaman Firamare, a gundumar raya kasa ta Panda, mai suna Malam Ibrahim Rabo, bayanai sun nuna cewa a sakamakon barazanar da ’yan uwan na sa su ka rika yi masa gabanin kashe shi, ya kai maganar wajen wani Baffansu mai suna Akwatirik, da kuma wajen Dagacin kauyen Gitata, amma har a wurare biyun, da-kyar ya kubuta daga hanun mutanen, inda suka yi masa duka bayan sun bar wajen, ba tare da nasarar sasantasu ba.
Wani abokin marigayin mai suna Ibrahim Tata ya bayyana wa Aminiya cewa marigayin, wanda shi kadai ne Musulmi a cikin ’yan uwan nasa, ta kai ga ya amince ya bada kansa don aikata wata al’ada irin tasu ta ‘yan kabilar Gwandara, wadda ke bukatar wanda a ke tuhuma da maita ya yi rantsuwa, don ganin ya wanke kansa daga tuhumar, amma sai ’yan uwan suka bayyana masa cewa ba makawa sai sun kashe shi.
A tattaunawar da Aminiya t ayi da matar marigayin, mai suna Malama Hadiza Ibrahim, wadda ta ce kusan shekara 20 ke nan take tare da shi, har suka samu ’ya’ya uku da suka hada da Ummi mai shekara 14, da Ganiya mai shekara 10, sai kuma Sibaratullahi mai shekara 6, ta bayyana cewa halin damuwa da ta samu kanta da marigayin, ya kaita ga shan azumi da dama na watan Ramadan da ya gabata tare da marigayin, inda a karshe suka yanke shawarar barin kauyen bayan mijin nata ya samu izinin sauyin wurin aiki daga sashen kula da ilimi na karamar hukumar Karu.
“Na samu damuwa matuka a sakamakon yadda dan uwansa da suke ’yan uba mai suna Kwando, da By Mistake, da mai-gashi ke barazana ga ransa, a nan suke zuwa har kofar dakinmu wannan na rike da adda, wannan da sanda, suna ikrarin cewa yana da maita sai sun kashe shi. Ya kalubalance su da su je wajen wani mai magani su sha kowa ya rantse, duk da kasancewarsa Musulmi, amma sai suka ki, suka ce ba makawa sai sun kashe shi.
“Abun ya damemu kwarai. mun yanke shawararar barin kauyen nan bayan Sallah da kwana daya, kuma a ranar ne ya je wajen wani da suka yi maganar zai sa yi mashin dinsa a kusa da kauyen nan, don ya samu guzurin tafiya, ni kuma na shirya ina jiran dawowarsa mu wuce, sai ga kaninsa mai suna Kwando ya zo da labarin cewa ai barayi sun kashe shi. ya dawo da mashin din da ya tafi da shi, wanda ya ce shi ne ya goyi marigayin a kan mashin din, amma sai barayin suka hau mijina da sara, shi kuma ya samu nasarar gudu da mashin din.
Wata makwafciyar iyalan, da ke haya a daya daga cikin dakunansu, mai suna Jummai Tanimu, ta ta’allaka daukacin rigimar a kan fili wanda kuma daga bisani ya kai ga gabar maita da suka dora masa. Jummai ta ce a al’adarsu ta Gwandara dukiyar da mahaifi ya bari ta daukacin dangi ce ba ta ’ya’ya ko iyaye ko mata ba kawai, kuma kasancewar marigayin shi ne babba a cikin ’ya’yan da mahaifinsu ya bari, ’ya’yan baffanai da sauran ’yan uwansa na yi masa zargin kankane dukiyar da mahaifinsu ya bari.
Shi kuwa abokin marigayin, Ibrahim Tata, cewa ya yi, marigayin gwagwarmayar kare dukiyar uban ya rikayi ba wawureta ba, inda ya yi misali da wani fili mai girman hekta kusan 100 da wani ya yi yunkurin kwace rabinsa, amma sai abokin nasa ya kai maganar kotu a garin Keffi, sai dai a sakamakon kashe kudi a lokacin shari’ar, ya yanki wani waje daga cikin filin ya sayar, inda kuma ya bai wa dan’uwansa Kwando wani kaso a cikin kudin, wanda ya yi amfani da shi wajen  gina dakuna 12 tare da sayen mashin.
Mahaifiyar Kwando da aka tuntubeta, ta ce ‘ba ta da ta cewa. ba a samu jin ta bakin dagaci ba, don a lokacin ba ya fadarsa ba ya nan, amma Ofishin ’yan sanda na garin Gitata sun tabbatar da faruwar lamarin, inda babbar jami’a a wajen O.C,  sun kama mutanen hudu da a ke zargi da kisan, inda aka mika su ga babban ofishinsu da ke garin Lafiya, don ci aba da bincike.