Ana zargin wata amarya da yi wa mijinta yankan rago
Yan sanda a Jihar Filato na rike da wata amarya mai suna Maryam Yahaya mai shekara 17, bisa zarginta da yi wa mijinta Muhammad Lawal Bala mai shekara 30 yankan rago. Wannan lamari ya faru ne a ranar Talatar makon jiya da misalin karfe 4.30 na yamma a Unguwar Gangare da ke Jos.Yayan marigayin, kuma […]

Yan sanda a Jihar Filato na rike da wata amarya mai suna Maryam Yahaya mai shekara 17, bisa zarginta da yi wa mijinta Muhammad Lawal Bala mai shekara 30 yankan rago.
Wannan lamari ya faru ne a ranar Talatar makon jiya da misalin karfe 4.30 na yamma a Unguwar Gangare da ke Jos.
Yayan marigayin, kuma shugaban kungiyar mahauta na Unguwar Gangare, Alhaji Hamza Dikko ya ce a ranar da lamarin y faru, “marigayin ya zo rumfata ya yi alwala muka yi Sallar Azahar tare. Daga nan ya sha fura a wajen wata Bafulatana ya dauki cefanensa ya shiga gida ya kwanta barci,” inji shi. Ya ce “Muna cikin Sallar La’asar a masallaci sai aka yi min waya cewa, na yi sauri ga Lawan a cikin jini. Kafin na isa sai na ga an riko wani dana yana kuka, na ce me ya faru sai ya ce ai har ya mutu.”
Alhaji Hamza ya ce tunda an ce an yanka shi ne a wuya saboda yana da hawan jini bai iya shiga dakin ya ga gawar ba. Sai ya tsaya a waje yana ba daruruwan matasan da suka yi cincirindo a kofar gidan hakuri. Ya ce da kyar aka samu hankali ya kwanta aka dauki gawar aka kai Asibitin Filato da ke Jos, aka ajiye. Ya ce washegari suka je aka ba su gawar suka yi mata jana’iza.
Ya ce an shaida masa cewa su biyu ne kawai a cikin dakin shi da matarsa a lokacin da lamarin ya faru. Kuma ba a ga wani ya gilma ta kofar gidan ba a lokacin. Ya ce akwai wata mata a gidan tana aikace-aikace a lokacin da abin ya faru. Don haka ake zargin matarsa wadda kwata-kwata watansu daya da aure da kashe shi.
Makwabtan marigayin sun bayyana wa wakilinmu cewa a lokacin da abin ya faru Maryam ta fito daga dakin tana ihu cewa Lawal ya yanka kansa. Suka ce marigayin ya fito daga cikin dakin rike da makogwaronsa jini na zuba kafin ya yanke jiki ya fadi.
Wani dan uwan marigayin, Muhammad Kabiru Usama ya ce marigayin ya sha wahala wajen daukar dawainiyar matar tasa kuma shi ne ya biya Naira dubu 20 kudin rubuta jarrabawar fita daga makarantar sakandire da ta yi a kwanakin baya.
Ya ce da yake marigayin na sana’ar fawa ne a kullum yana ba mahaifiyar matar tasa bashin nama na Naira 1,500 tana sayarwa sai wata take biyansa. Domin tana abincin sayarwa a gidansu. Ya ce da maganar aurensu ta taso aka yanka masa sadakin Naira dubu 50 ya biya aka daura.
Wasu na kusa da marigayin sun bayyana wa wakilinmu cewa Maryam ta yi ta nuna wa marigayin kiyayya bayan da aka yi auren.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Felicia Anslem ta shaida wa wakilinmu cewa, a binciken farko da suka gudanar kan al’amarin matar ta tabbatar da cewa ita ce da kanta ta yanka mijinta da wuka. Ta ce sun tura wannan magana zuwa sashin binciken aikata manyan laifuffuka na CID domin ci gaba da bincike. Kuma da zarar sun kammala binciken za su gabatar da ita a gaban kotu.