Ana zargin wata daliba da batanci ga Manzon Allah a Borno
Ana zargin dalibar Kwalejin Kimiyya ta Ramata da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) a Facebook.
Ana zargin wata daliba a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Ramat da ke Maiduguri a Jihar Borno Naomi Goni, da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) a Facebook.
A safiyar Litinin dandazon jama’a sun yi dafafi a ofishin Rundunar ta Bakwai ta Sojin Najeriya da ke Maiduguri domin nuna fushinsu kan katobarar da dalibar ta aikata.
- 2023: Zan goyi bayan duk dan takarar da PDP ta tsayar – Bala Mohammed
- Batanci ga Annabi: Kura ta fara lafawa a Sakkwato
Da take magana kan zargin batancin da ake wa Naomi Goni, Kungiyar Kare Hakkoki ta Musulunci (MURIC) ta bukaci jama’a kada su dauki doka a hannunsu, su bari ’yan sanda su dauki matakin da ya dace.
Daratan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi kiran a ranar Lahadi da dare inda ya ce, “An samu rahoton cewa wata matashiya ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Borno.
“Wadda ake zargin ita ce Naomi Goni, daliba a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ramat da ke Maiduguri.
“Wani Abdulmajid Tanko Izge ne kan gaba da zargin cewa, ‘Akwai wata mai suna Naomi Goni da ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW); a Musulunci hukuncin kisa ne ko da kuwa Musulumi ne ya aikata.
“‘Muna kira ga Gwamnatin Jihar Borno ta da ta gaggauta daukar matakin da ya dace, idan ba haka ba Musulmi ba za su natsu ba, za mu dauki mataki’.”
Amma daraktan na MURIC ya ce “Amma daga sakon Abdulmajid Tanko zuwa sauran, babu wanda ya nuna hakikan kalaman batancin [da suke zargin Naomi] ba.
“Saboda Masu zargin sun fito su bayyana wa ’yan Najeriya hakikanin abin da suke ganin batanci ne.
“Hasali ma, ita wadda suke zargi da wannan katobara ta musanta abin da ake tuhumar ta da aikatawa, cewa kutse aka yi a wayarta a shekarar da ta gabata.
“Wannan ya sanya ayar tambaya a kan zargin, ya kuma bambanta zargin da ake mata, domin akwai yiwuwar ba ita ta yi ba.”
Ya kara da cewa, “Ya ce kudin goron da Abdulmajid Tanko ya yi cewa ‘a Musulunci hukuncin kisa ne ko da kuwa Musulumi ne ya aikata,’ abin damuwa ne ga masana shari’ar Musulunci saboda bai bambance tsakanin laifin da Musulmi ya aikata daga wanda Kirista ya aikta ba,” inji Farfesa Akintola.
Zargin Naomi Goni da batancin na zuwa ne a yayin da ake kokarin shawo kan rikicin da ya biyo bayan batancin da wata daliba, Deborah Samuel, ta yi wa Manzon Allah (SAW), a Kwalejin Ilimi na Shehu Shagari da ke Jihar Sakkwato.
Farfesa Akintola ya bayyana cewa sannan abu ne a bangaren Shari’a cewa a Najeriya ba za a iya gurfanar da Kirista a kotun Musulunci ba, sai dai idan ita da kanta ta zabi kotun Musulunci; sannan a kotun zamani ake gurfanar da Kirista.
“Shi ya sa ya kamata Musulmin Jihar Borno su bar ’yan sanda su bincike kes din Naomi.
“Ita Kirista ce, kuma muna da hukumomin tsaro da za su dauki mataki da ya dace domin gano ko da gaske ta aikata batanci,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga malaman Musulunci a Jihar Borno da su bi matakan da suka dacewa, yana mai cewa ya kamata a rika yi wa matasa tarbiyar da ta dace.
A cewarsa, “A bari ’yan sanda su yi bincike, sannan ya kamata matasa su samu kwarin gwiwa game da gwamnati, kada su ji wata tantama cewa ’yan sanda za su goyi bayan Naomi.
“Muna da gwamna mai takawa, Farfesa Zulum zai tabbatar da adalci, kan duk wanda aka samu da laifi.
“Muna kuma kira ga ’yan sanda da su gudanar da cikakken bincike a fili, kuma sakamakon binciken farko da aka fitar zai ba wa mutane kwarin gwiwa.”