Ana zargin wata mata da satar talabijin a Gombe
An kama wani matashi kan zargin satar kayayyakin abinci a shagon wani mutum a Gomben.
’Yan sanda sun cafke wata mata da ake zargi da satar akwatin talabijin a gidan wata mata da ke unguwar Tumfure ta Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe.
Kakakin ’yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana hakan yayin gabatar da wadda ake zargin ga manema labarai.
- Gwamnati za ta bai wa ma’aikata tallafin rage raɗaɗi a Yobe
- An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja
ASP Mahid ya bayyana cewa ana zargin matar ta sato akwatin talabijin din bayan ta fasa gidan matar mai suna Zulaihat Garba Saleh.
Kazalika, ASP Mahid ya ce ’yan sanda sun cafke wani matashi kan zargin fasa shagon wani mutum mai suna Babayo Bilal a unguwar Shango Jauro da ke jihar.
Jami’in hulɗa da al’umma na rundunar ’yan sandan ya ce matashin da ake zargi mai shekaru 39 ya saci kayayyakin abinci da kuɗin da suka kai naira 35,200.
Ya shawarci mazauna unguwar da su riƙa kaffa-kaffa da dukiyarsu tare da neman su ci gaba da kai wa mahukunta mafi kusa rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
Tuni dai ababen zargin sun soma bai wa ’yan sanda haɗin kai kan laifin da ake zarginsu, lamarin da ASP Mahid ya ce da zarar sun kammala bincike za a tura su Kotu.