Ana zargin ’yan banga da kashe mutum 16 a Jihar Sakkwato

Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da kashe mutum 16 da kungiyar ’yan banga ta yi a karamar Hukumar Rabah da ke Jihar Sakkwato a ranar Lahadin da ta gabata. Ana zargin ’yan kungiyar sun gayyato wasu takwarorinsu ne daga Jihar Zamfara don su taya su neman wasu mutane da sukA kira barayi, a […]

Ana zargin ’yan banga da kashe mutum 16 a Jihar Sakkwato
Ana zargin ’yan banga da kashe mutum 16 a Jihar Sakkwato

Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da kashe mutum 16 da kungiyar ’yan banga ta yi a karamar Hukumar Rabah da ke Jihar Sakkwato a ranar Lahadin da ta gabata.

Ana zargin ’yan kungiyar sun gayyato wasu takwarorinsu ne daga Jihar Zamfara don su taya su neman wasu mutane da sukA kira barayi, a yayin da suka samu nasarar iske mutanen a cikin kauyuka sai kawai suka auka musu da sara da adda har suka kashe mutum 16.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Sakkwato Shu’aibu Lawai Gambo ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan lamarin.
Shu’aibu Gambo wanda yayi tir da lamarin ya ce sun kama mutum 10 daga cikin ’yan bangar da ake zargi da yin aika-aikar kuma rundunarsu za ta mika su ga kotu bisa zargin kisan kai. “Wannan lamarin da ke faruwa a yanzu ’yan banga su je kama mutane su yi musu hukunci ya saba wa doka, kuma ba za mu lamunce shi ba. Idan dan banga ya kama mutum ba wanda ya ce ya yi masa hukunci dole ne ya mika shi ga hukuma,” inji Kwamishinan.
Ya kara da cewa, “Wannan kazamin yanayi da zai sanya masu aikin sa-kai mika goron gayyata ga wasu mutane da ke wajen jiha su zo don taya su aikin saba doka, ’yan sanda ba za su lamunci hakan ba, kuma ba wani dan banga da zai gayyaci dan uwansa a wajen jiha ba tare da sanin shugaban ’yan sandan yanki (DPO) ko shugaban karamar hukuma ba.”
Kwamishinan ya ce suna farin ciki da kungiyoyin banga da masu hada hannu da hukuma don magance miyagun ayyuka, sai dai ya kamata duk masu son kafa wata kungiyar banga ko ta sa-kai, su tuntubi ’yan sanda don nuna musu yadda ya kamata su gudanar da ayyukansu bisa tanadin doka.