Ana zargin ’yan bijilanti da kashe Fulani 10 ’yan gida ɗaya a Jihar Oyo

Tun daga ranar da aka kawo wannan hari muke zaman makoki a ƙauyen Gbepakan.

Ana zargin ’yan bijilanti da kashe Fulani 10 ’yan gida ɗaya a Jihar Oyo

A tsakiya Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo ne CP Adebola Hamzat a lokacin da yake yi wa ‘yan jarida bayani a ofishinsa a Ibadan

Kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Oyo ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Oyo da Sufeto-Janar na ’Yan sanda su hanzarta daukar matakin gano mutanen da suka yi wa Fulani 10 ’yan gida daya kisan gilla cikin daren ranar Talata a ƙauyen Gbepakan da ke Ƙaramar Hukumar Saki ta Yamma a Jihat Oyo.

Shugaban Ƙungiyar Alhaji Ibrahim Jiji ne ya yi kiran a hirar da ya yi da Aminiya jim kadan bayan gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar fara bincike a kan lamarin.

Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Bayo Lawal wanda yake tare da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Sonubi Ayodele ya jagoranci ayarin manyan jami’an gwamnati inda suka ziyarci ƙauyen Gbepakan a ranar Alhamis don gane wa idanunsa irin ɓarnar da aka yi wa Fulanin.

Ya yi tir da Allah-wadai da irin ɓarnar da aka aikata. Ya ce Gwamnatin Jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta yi wa al’ummomin jihar alƙawarin kariyar tsaron rayuka da kadarorinsu domin samar da zaman lafiya da ci gaba.

Ya ce, tuni gwamnati ta fara bincikar wannan ƙazamin lamari domin gano wadanda suka aikata shi da a hukunta su.

Mataimakin Gwamnan ya jajanta wa al’ummar Fulanin tare da roƙon su kwantar da hankali domin yanzu haka ’yan sanda suna binciken ƙwaƙwaf domin gano ainihin musabbabin aukuwar lamarin.

Alhaji Ibrahim Jiji shi ne ya jagoranci ayarin Mataimakin Gwamnan zuwa cikin gidan da maharan suka shiga suka yi wannan danyen aiki.

Alhaji Jiji ya ce, “Cikin dare ranar Talata da ta gabata ce mutanen da muke zargin ’yan bijilanti ne suka kai hari a gidan a lokacin da iyalan magidanta biyu ’yan uwan juna wa da ƙane suke barci inda suka kama su da sara da manyan makamai har da bindiga ba gaira ba dalili.”

Ya ce, a nan take mutum 10 da suka hada da tsofaffi maza da mata da ƙananan yara suka rasu. Sauran mutanen da suka samu raunuka yanzu haka suna kwance a Asibitin Baptist da ke garin Saki inda likitoci suke ƙoƙarin ceto rayukansu.

Da yake amsa tambaya, ya ce “Haka kawai aka kai wa wadannan bayin Allah hari suna barci a gidansu.

“Babu wata matsala ta rikicin manoma da makiyaya ko zargin Fulani da aikata wani abu.

“A bara ma an kai irin wannan hari a garin Iganna inda aka ƙone gidajen Fulani da wasoson dukiyarsu.

“Matakin farko da muka dauka a kan wannan hari na ƙauyen Gbepakan shi ne roƙonjama’armu a Jihar Oyo su yi haƙuri da wannan jarrabawa da Allah Ya saukar masu kuma kada su kuskura su dauki doka a hannu.

“Mun miƙa wannan lamari baki daya ga Allah (TWT) kuma muna jiran sakamakon binciken da mahukunta ke yi,” in ji shi.

Alhaji Ibrahim Jiji ya nuna matuƙar baƙin ciki kan yadda wasu kafofin yada labarai a Jihar Oyo suka ƙi ba da wannan labari mai muhimmanci domin sanar da duniya irin ɓarnar da aka yi wa Fulani a ƙauyen Gbepakan.

Ya ce “Kamata ya yi ku zo mu yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Oyo da ƙasa baki daya.”

Ya ce Ƙungiyar Miyetti a Jihar Oyo ta jinjina wa Mataimakin Gwamnan Jihar Bayo Lawal kan hanzarta kai ziyarar gani da ido da ya jagoranci ayarin mahukuntan jihar zuwa ƙauyen da lamarin ya auku.

Ɗaya daga cikin dangin mamatan daakasakayasunansa ya ce “Mun yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Tun daga ranar da aka kawo wannan hari muke zaman makoki a ƙauyen Gbepakan.

“Ba mu taɓa ganin irin haka a baya ba. Wallahi cikin dare suka shigo dauke da makamai suka yi wa mutanen da suke kwance a gidan dirar mikiya suka karkashe su kamar dabbobi.”

A yayin da Aminiya ta nemi jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso kan wannan lamari da halin da ake ciki a ƙauyen Gbepakan, bai amsa kiran waya ba.

Sai dai wata majiyar ’yan sanda ta ce “Tun ranar da lamarin ya auku Kwamishinan ’Yan sanda Sonubi Ayodele ya girke jami’ansa a ciki da wajen ƙauyen.

“Kuma ina tabbatar maka cewa binciken da ake yi ya fara haifar da da mai ido,” in ji majiyar.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda