Ana zargin ’Yan kato-Da-Gora da kisan wani yaro
A ranar Litinin da ta wuce ne iyayen wani saurayi dan shekara 14 mai Suna Zakariya Adamu suka zargi wasu matasa ’Yan kato-Da -Gora da halaka shi. Lamarin ya auku ne da misalin karfe 4:00 na yamma a ranar bayan ’Yan-kato-Da-Gorar sun kama saurayin a cikin makarantar ’Yan mata da ke Unguwar Ma’azu.Majiyoyinmu sun ce, […]
A ranar Litinin da ta wuce ne iyayen wani saurayi dan shekara 14 mai Suna Zakariya Adamu suka zargi wasu matasa ’Yan kato-Da -Gora da halaka shi. Lamarin ya auku ne da misalin karfe 4:00 na yamma a ranar bayan ’Yan-kato-Da-Gorar sun kama saurayin a cikin makarantar ’Yan mata da ke Unguwar Ma’azu.
Majiyoyinmu sun ce, babu wanda ya san dalilin kama saurayin a lokacin da ’Yan kato-Da-Gorar suka kai same cikin makarantar.
Yayan marigayin, Baba Adamu wanda ya ce yaron ya rasu ne bayan duka da dauri da ’Yan kato-Da- Gorar suka yi masa. “Ba na gida a lokacin da abin ya faru, sai kawai aka kira ni ta waya cewa an kama Zakari. Da na je ofishin ’Yan kato-Da Gora na Unguwar Ma’azu sai na tarar da shi a daure ko motsawa ba ya yi. Ban kunce shi ba har sai dai babbansu ya shigo ofishin ina jin lokacin da yake tambayar su wa suka buge shi tare da yi masa irin wannan dauri. Ni kuma ina tsaye ina kallonsu har sai da suka kunce shi daga nan suka watsa masa ruwa domin ya farfado. Da suka lura ba ya motsi sai suka dauke shi zuwa wani asibiti mai suna Al’amin. A can ne aka duba shi aka ce ai tuni ya rasu. Gaskiya rasuwarsa ta tayar mana da hankali, domin yaro ne karami kuma ba mu san laifin da ya yi suka kasha shi ba,” inji yayan.
Baba Adamu ya bukaci Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya kawo masu dauki domin ba za su yarda a kashe masu dan uwa ba babu laifin fari bare na baki ba. “Muna neman adalci daga rundunar ’yan sanda a kan wannan zance. Mun ji cewa sai da suka yi masa bulala kusan 50 kafin su daure shi. A yanzu haka ofishin ’Yan kato-Da-Gorar a rufe yake babu kowa tunda lamarin ya faru,” inji shi.
kokarin da Aminiya ta yi don ji daga bakin mahaifiyar marigayin ya ci tura domin an ce an kai ta asibiti saboda kaduwa da ta yi kan kasha danta.
Bayanan da Aminiya ta samu shi ne ’yan sanda sun kama uku daga cikin ’Yan kato-Da-Gorar da ake zargi da dukan marigayin har ya yi sanadin rasuwarsa.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Zubairu Abubakar bai amsa waya ba.