Ana zargin ’yan sanda da jikkata dillalin fili a Abuja

Wani dillalin fili mai suna Adamu Dahiru da ke garin Deidei, Abuja ya samu rauni bayan da aka zargi wadansu ’yan sanda uku da yi masa duka, kan rigimar fili a tsakaninsa da daya daga cikinsu a garin Dakwa na Birnin Tarayya, Abuja. A zantawarsa da Aminiya, dillalin ya ce kamar shekara dya ke nan […]

Ana zargin ’yan sanda da jikkata dillalin fili a Abuja

Adamu Xahiru dillalin fili da ake zargin ‘yan sandan sun jikkata

Wani dillalin fili mai suna Adamu Dahiru da ke garin Deidei, Abuja ya samu rauni bayan da aka zargi wadansu ’yan sanda uku da yi masa duka, kan rigimar fili a tsakaninsa da daya daga cikinsu a garin Dakwa na Birnin Tarayya, Abuja.

A zantawarsa da Aminiya, dillalin ya ce kamar shekara dya ke nan ya sayi filin daga hannun wani mai suna Malam Ahmadu na Kwana, da shi kansa ya sayi fulotin daga wajen asalin mai shi, mai suna Jihadi. Ya ce kamar wata 7 da suka gabata bayan ya kafa tubali a filin, sai wani ya tunkare shi cewa wajen nasa ne. “To ana cikin haka sai wani dan sanda Gambo ya ce ya amshi rigimar kuma  ya sayi filin daga wajen wanda nake takaddama da shi.

“Ya nemi mu je wajen shugaban ’yan sanda na karamin ofishinsu da ke Dakwa, muka je kuma na gabatar musu da wanda ya sayar mini da fili, inda ya tabbatar da cewa lallai shi ya sayar mini da filin, sai dai ya shaida masa cewa Jihadi ne asalin mai filin. Da farko ya fara cinikin fulotin ne da wancan mutum, amma saboda bai biyan dukkan kudi ba, kuma bukata ta bijiro, sai ya sayar da wajen ga wanda ya sayar mini,” inji shi.

Ya ce “Sai dai kamar yadda ya bayyana bai mayar masa da kudinsa da ya fara ba shi ba. To shi ne sai aka bukaci gaba daya mu dakatar da aiki a wajen, sai an warware takaddamar. To ana cikin haka a ranar Asabar da ta gabata sai aka bukaci in zo wani fili da ake bukata da ke kusa da wurin, saboda ni dillali ne. Bayan isowata mun fara magana, sai kawai na ga dan sanda Gambo da wadansu abokan aikinsa biyu da kuma wadansu matasa suka zo wurin. Da farko ya bukaci in zo, ina zuwa sai suka fara yi min tambayoyi tare da buguna. Tun ina iya magana har na daina na fadi kasa, amma ba su daina buguna ba wadansu na tattaka ni.”

“Wayoyina biyu da kudin da ke aljihuna duk na rasa a wajen. Bayan nan sai suka dauke ni a motarsu kan za su kai ni ofishin ’yan sanda na SARS inda suke aiki, amma sai suka sauya shawara suka kai ni karamin ofishin ’yan sanda na garin Deidei wajen shugabansu. Da farko ya nuna kaduwarsa a kan halin da ya gan ni a ciki, nan take ya ce da su ba zai karbe ni ba, su  kai ni asibiti. Amma maimakon hakan sai ya kai ni  babban ofishin ’yan sanda na Zuba, a can ma DPO ya ce lallai ya kai ni asibiti. To a nan ne ya kai ni wani shagon magani aka ba ni magani bayan nan na dawo gida. An kawo mai dori da mai kaho aka yi mini, sai dai saboda jikina na ciwo ko’ina, sai mutanena suka kawo ni wannan asibiti, ana  min jinya,” inji shi.

Da aka tuntubi DPO din ’yan sandan Zuba, CSP Muhammad Yahaya, ya tabbatar da faruwan lamarin. Ya ce dan sandan mai suna Sufeto Gambo Kawu na aiki ne da sashin yaki da manyan laifuffuka (SARS) da ke Abuja shi da abokan aikinsa biyu da ake zargin da hannu a lamarin. Ya ce tuni aka sanar da babbar ofishinsu na Abuja kuma daga can ne za a yanke shawarar inda za a binciki al’amarin inji shi.