Ana zargin ’yan sanda da kashe makiyaya biyu a kan Naira 50

Hedkwatar ’Yan sandan Jihar Adamawa da ke Yola ya tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu makiyaya a karamar Hukumar Toungo ta jihar, inda aka yi zargin cewa an yi kashe makiyaya ne sakamakon cacar baki da ta barke a tsakanin makiyayan da ’yan sanda a kan Naira 50 kacal.DSP Usman Abubakar ya tabbatar da kama […]

Ana zargin ’yan sanda da kashe makiyaya biyu a kan Naira 50
Ana zargin ’yan sanda da kashe makiyaya biyu a kan Naira 50

Hedkwatar ’Yan sandan Jihar Adamawa da ke Yola ya tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu makiyaya a karamar Hukumar Toungo ta jihar, inda aka yi zargin cewa an yi kashe makiyaya ne sakamakon cacar baki da ta barke a tsakanin makiyayan da ’yan sanda a kan Naira 50 kacal.
DSP Usman Abubakar ya tabbatar da kama ’yan sandan a lokacin da suke sintiri. “Hakika mun samu labarin faruwar lamarin kuma an kama wadanda ake zargi da aikata wannan danyen aiki kuma tuni ana gudanar da bincike,” inji shi.
Magana a madadin shugaban Miyetti Allah, Malam Sanusi Bara, ya shaida wa manema labarai a Yola cewa ba don Allah Ya sa manya sun sa baki a maganar ba da lamarin zai iya haddasa rigingimu da dama. Malam Sanusi Bara ya ba da sunayen makiyayan da aka kashe da cewa su ne Jibo da Maikudi. Ya ce an samu ramukan harsasai biyar a jikin Jibo, uku a jikin Maikudi, kuma ana bincike a kan faruwar hakan.
Malam Bara ya ce “Rasuwar Jibo ya sanya karin dawainiya ga mahaifinsa Malam Dawa Musa domin ya rasu ya bar mata da ’ya’ya biyu. Maikudi kuma na shirin yin aure ne hakan ta faru da  shi.”
Idan ba za a manta ba kwanakin baya wani abu makamancin hakan ya faru inda aka kashe Fulani 25 a kauyen Bali a karamar Hukumar Demsa.
A yanzu dai ana zaman dar-dar a Toungo domin Fulanin sun ce za su dauki fansa idan har hukuma ba ta dauki mataki a kan lamarin ba.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista