Ana zargin yaron shago da kwashe Naira miliyan 18

An gurfanar da wani matashi mai suna Sani Usman Kura wanda aka fi sani da Koc 4 a gaban Kotun Majistare ta 12 da ke Nomanslan a birnin Kano bisa zarginsa da da yi wa shagon maigidansa wawaso. Ubangidan matashin mai suna Dauda Ali Kura ne ya yi karar yaron nasa a gaban kotun, inda […]

Ana zargin yaron shago da kwashe Naira miliyan 18

Nkanu Onnoghen

An gurfanar da wani matashi mai suna Sani Usman Kura wanda aka fi sani da Koc 4 a gaban Kotun Majistare ta 12 da ke Nomanslan a birnin Kano bisa zarginsa da da yi wa shagon maigidansa wawaso.

Ubangidan matashin mai suna Dauda Ali Kura ne ya yi karar yaron nasa a gaban kotun, inda ya gano cewa ya kwashe masa har Naira miliyan 18.

Sai dai lokacin da dan sanda mai gabatar da kara Saje Jacob Solomon ya karanto wa wanda ake zargi takardar karar da ake masa, ya musanta aikata laifin cin amana da zamba, wanda ya saba wa sashe 311 na Kundin Shari’a na Final Kod. Alkalin Kotun Mai shari’a Muntari Dandago ya dage sauraren karar zuwa ranar 29 ga wannan wata na Oktoba domin fara sauraren shaidu.