Ana zargin yaron shago da zambar Naira miliyan 25

  Babbar Kotun Majistare Mai lamba 28 da ke Gyadi-Gyadi ta fara sauraren karar da aka kai wani matashi mai kimanin shekara 27 mai suna Musbahu Auwalu na Unguwar Agadasawa a birnin Kano bisa zarginsa da zambar Naira miliyan 25. Mai gabatar da kara Saje Sadik Na’abba ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin […]

Ana zargin yaron shago da zambar Naira miliyan 25

 

Babbar Kotun Majistare Mai lamba 28 da ke Gyadi-Gyadi ta fara sauraren karar da aka kai wani matashi mai kimanin shekara 27 mai suna Musbahu Auwalu na Unguwar Agadasawa a birnin Kano bisa zarginsa da zambar Naira miliyan 25.

Mai gabatar da kara Saje Sadik Na’abba ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya ci amanar ubangidansa Alhaji Usman Warshu wanda ya dauke shi aikin yaron shagonsa mai suna Baby Dream Center da ke Titin Sabon Titin Mandawari. “Ka dauki tsawon shekara goma kana shagon inda ya amince maka kana sayar da  kayayyaki na miliyoyin Naira. Sai dai  a wannan lokaci yake zargin ka yi masa zambar kudin kayayyakin da ka sayar har na Naira miliyan 25 ka mayar da kudin suka zama naka,” inji mai gabatar da karar.  

Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifuffukan da suka hada da zamba cikin amici da cuta da sata da mai gabatar da kara ya ce sun saba wa sashe na 308 da 312 da 320 na kundin Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Hajara Garba ta bayar da belin wanda ake zargi kan Naira dubu  50 da mutum biyu da za su tsaya masa inda ta dage shari’ar zuwa yau Juma’a.

A wani labarin kuma Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge Waje a birnin Kano ta daure wani matashi bisa samunsa da laifin satar wayar dan sanda a ofishin ’yan sanda na Hotoro.

Da sanda mai gabatar da kara,  ASP Shehu Adamu ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin Abba Abubakar ya sace wayar wani dan sanda mai suna Saje Nasiru Yahaya a ofishinsu na Hotoro.

’Yan uwan Abba ne suka kai kararsa ofishin ’yan sanda na Hotoro, kuma a daidai lokacin da ake sauraron bayanansu ne sai matashin da ya sace wayar dan sandan da ke daukar bayanan nasu.

Bayan karanto zargin Abba ya amsa laifinsa, laifin da mai gabatar da kara ASP Shehu Adamu ya ce ya saba wa sashe na 286 na Kudin Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Nasir Abba Magashi ya daure matashin a kurkuku na wata hudu ko ya biya tarar Naira dubu 20.