Ana zarginsa da kashe dansa saboda yi masa kashi a daki
Wani magidanci mai suna Mista Johnson da ke zaune a Unguwar Idu- Gwari a garin Karmo a Birnin Tarayya, Abuja, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe dansa saboda ya yi masa kashi a cikin daki da daddare.Magidancin wanda aka kubutar da shi da kyar daga fusatattun jama’a, bayan da aka gano gawar dan […]
Wani magidanci mai suna Mista Johnson da ke zaune a Unguwar Idu- Gwari a garin Karmo a Birnin Tarayya, Abuja, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe dansa saboda ya yi masa kashi a cikin daki da daddare.
Magidancin wanda aka kubutar da shi da kyar daga fusatattun jama’a, bayan da aka gano gawar dan nasa a gidan, ana zargin ya kashe yaron ne mai suna Prmise Johnson mai shekara bakwai saboda ya yi kashi ya kunshe a cikin leda ya ajiye a karkashin gadon mahaifin lokacin da suke barci cikin dare.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata, Aminiya ta samu labarin cewa bayan magidancin wanda ke tare da amaryarsa da dansa Promise Johnson, ya yi wa yaron duka da sanda sai ya kai shi inda ake ajiyar itace, ya komo daki ya bar shi yashe. Majiyarmu ta ce da gari ya waye ne wata mace ta ga yaron a yashe, ta ankarar da mazauna gidan hayan, wadanda suka lura ya riga ya mutu.
Wata ’yar haya a gidan da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa Mista Johnson ya zo gidan ne kamar wata hudu da suka gabata, kuma ya samu matsala da inda yake aikin leburanci kamar mako daya, kuma ya jima da rabuwa da mahaifiyar yaron. ’Yan sandan Karmo sun wuce da mutumin da matarsa wadda ita ma ake zargi da kuntata wa yaron a lokuta da dama.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, DSP Hyelira Altine Daniel ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce mutumin ya amince da aikata laifin kuma ana ci gaba da bincike, sai dai ta ce bayanai sun nuna cewa yaron na fama da ciwon farfadiya.