Ana zarginsa da kashe mai neman matarsa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wani manomi mai suna Ahmed Magaji da ke garin Kabo a Jihar Kano bisa zarginsa da laifin kashe wani mai suna Ibrahim Yakubu da yake zargin da neman matarsa. Manomin mai shekara 40 ya bayyana wa manema labarai cewa duk da cewa marigayin ya dade yana kokarin neman […]

Ana zarginsa da kashe mai neman matarsa
Ana zarginsa da kashe mai neman matarsa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wani manomi mai suna Ahmed Magaji da ke garin Kabo a Jihar Kano bisa zarginsa da laifin kashe wani mai suna Ibrahim Yakubu da yake zargin da neman matarsa.

Manomin mai shekara 40 ya bayyana wa manema labarai cewa duk da cewa marigayin ya dade yana kokarin neman matarsa ta kai ya yi kokarin yi mata fyade kimanin sau hudu, amma ba shi ya kashe shi ba. “Babu shakka duk da wannan mutum ya dade yana neman matata, domin a wasu lokutan ya so ya yi mata fyade, amma ba ni na kashe shi ba. Al’ummar unguwarmu ne ke da alhakin hakan. Da ma jama’ar unguwarmu suna jin haushinsa game da abin da yake yi a unguwar kasansacewar ba gidana kadai yake shiga ba, domin a wasu lokutan yakan shiga gidajen matan aure ya zare musu wuka ya yi musu fyade,” inji shi.
Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, manomin ya ce mutumin ne ya zo gidan don yi wa matarsa fyade inda tsautsayi ya gitta jama’ar unguwar suka kashe shi. “Ranar da wannan lamari ya faru da ya zo gidana kamar yadda ya saba da niyyar yi wa matata fyade, to sai ya yi rashin sa’a matata ba ta nan. Lokacin da ya shigo daki ina barci sai kawai ji na yi ana shasshafa ni da yake ba mu da wutar lantarki a zatonsa matata ce. Jin haka da na yi ni kuma sai na cafke hannunsa sannan na yi ihu. Hakan ya jawo jama’ar unguwar da suka zo kawo min dauki suka yi masa a tare a karshe ya yi sanadiyyar
mutuwarsa,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya ce tuni rundunar ta fata bincike kan faruwar lamarin, inda ya ce da zarar bincikensu ya kammmala za su gurfanar da wanda akr zargi gaban kotu.
Ya yi kira ga jama’a su daina daukar doka a hannunsu, “Koda an kama shi da laifin fyade bai kamata a kashe shi ba, kamata ya yi da aka kama shi, sai a mika shi ga ’yan sanda ko shugabannin al’umma,” inji shi.