Ana zarginsa da kashe maigadinsa, da yanke sassan jikinsa

A ranar Alhamis din makon jiya ne aka tsinci gawar wani maigadi a wurin aikinsa an cire wasu daga cikin sassan jikinsa.Maigadin mai suna Adamu Jibirin mai kimanin shekara 25 da ke zaune a Unguwar Fatika da ke cikin garin Zariya, an samu gawarsa ce a gidan da yake gadi na wani dan kabilar Ibo […]

Ana zarginsa da kashe maigadinsa, da yanke sassan jikinsa

Marigayi Adamu Jibrin Maigadin da ake zargin maigidansa da kashe shiA ranar Alhamis din makon jiya ne aka tsinci gawar wani maigadi a wurin aikinsa an cire wasu daga cikin sassan jikinsa.
Maigadin mai suna Adamu Jibirin mai kimanin shekara 25 da ke zaune a Unguwar Fatika da ke cikin garin Zariya, an samu gawarsa ce a gidan da yake gadi na wani dan kabilar Ibo mai suna Henry da ke sayar da kayan mota a tsohuwar Kasuwar danmagaji a Marabar Wusasa, Zariya.
kanen mahaifin marigayin mai suna Gambo Adamu ya shaida wa wakilinmu cewa, “Muna zaune a gida sai Mai Unguwar Kuregu ya yi waya cewa an kashe Adamu don haka mu zo, sai aka tambaye shi sun yi fada ne? Sai ya ce a’a, mu dai zo. Sai muka dauki mota biyu da duk kusan mutanen gidanmu muka tafi da makara. Koda muka isa sai muka ga ’yan sanda a gidan da yake gadi a can Unguwar Kuregu da ke Wusasa, aka bude mana kofa muka shiga aka bude wani daki, aka kara bude mana wani dakin har sai da aka bude kofofi uku kafin muka ga gawar Adamu a kwance an yanka shi har ya fara wari, kuma muka ga ba idanunsa biyu an kwakule, kuma an fafe cikinsa, an yanke nononsa biyu.”
Ya ce haka suka dauko shi domin ganin yadda yake har ya fara zama wani iri sai shugaban ’yan sandan yankin ya ce su je su yi masa sutura.
Malam Gambo ya ce bayan dauko gawar marigayi Adamu zuwa gida sai suka ga ashe ba idanunsa kawai aka kwakule ba har cikinsa aka fasa aka cire zuciyarsa da kodarsa, an kuma yanke mazakutarsa, an huda wajajen kafadunsa, an yanke harshensa an cire makogoronsa.
Ya ce duka-duka da fara aikin marigayin kwana biyar wannan lamari ya faru da shi, “Da ma yana sana`ar tukin mota ce kuma wannan dan kabilar Ibo yana daukarsa shata yana dauko masa kaya daga Kaduna kuma ba yan ya rasa mota sai suka ci gaba da hulda,” inji shi.
Ya ce marigayi Adamu ya bar gida ranar Alhamis da misalin karfe 11:00 na rana, kuma a ranar Juma’a da misalin karfe 9:00 na dare aka sanar da su abin da ya faru.
Malam Gambo Adamu ya ce bayan sun yi wa marigayin sutura sai ga Mai unguwar Kuregu ya zo tare da Henry wai ya yi belinsa ya kawo shi ya yi musu ta’aziyya, sai Mai unguwar ya kama yi musu lacca wai ai dama yana jira ne ya tare a gidan sannan ya saya wa marigayi Adamu mota.
Ya ce “Amma shugaban ’yan sandan ya kira ’yan uwana sun tafi Kaduna tare da Henry din domin gudanar da bincike, mu kuma abin da muke so a yi, shi ne lallai ne hukuma ta tabbatar ta gudanar da bincike a kan wannan lamari, domin a lokacin da muka je dauko gawar marigayin abin da na lura shi ne duk kofofin da aka bude mana ba wadda take bude mabudi aka sa aka bude kuma daga marigayi sai shi maigidan kawai suke da mabudin dakunan. Don haka ta ina aka shiga har aka yi wannan danyen aiki? Mu a gaskiya wannan maigidan nasa muke zargi.
Mai Unguwar Kuregu Muhammadu Ahmad Amfani ya shaida wa Aminiya cewa “ina zaune a gida a ranar Juma’a 18/10/2013, misalin karfe 8:00 na dare sai na ji ana sallama, ina fitowa sai na ga jami’an tsaro suka ce DPO ne ya turo su domin su zo in kai su gidan wani wai shi Henry wanda ya je ya shaida musu cewar ya ga gawar mai gadinsa a cikin gidansa. Shi ke nan muka je gidan, to ana bude kofar shiga cikin falo to a wani daki kusa da dakin cin abinci sai muka ga gawar marigayi a kwance. Lallai da ni da wani jami`in ’yan sanda mai suna Oladipo da wani mai daukar hoto mu uku muka iya shiga dakin kuma a lokacin na ga shaidar yanka a wuyansa kuma babu riga a jikinsa kuma na ga an kwakule idanunsa, kuma na ga an bude cikinsa amma ban iya tabbatar da abinda aka cire a cikinsa ba. Daga ganin wannan hankalina ya tashi sai na fito waje domin abin ba kyan gani.
Mai Unguwar ya ce haka bai taba faruwa a unguwar ba kuma bai san shi Henry ba kuma ko da ya sayi filin ba ma shi ya kai takardar filin ya sa masa hannu ba, don haka ba zai shaida komai a kansa ba.
Wata majiyar ’yan sanda mai tushe da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce an kama mai gidan kuma yanzu haka an aika da shi Kaduna domin gudanar da bincike.