Ana zarginsa da sakin matar abokinsa
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Shahuci a Kano ta umarci ’yan sanda su tsare wani mutum mai suna Karibu Yahaya bisa zarginsa da sakin matar abokinsa ta waya. Dan sanda mai gabatar da kara Auwalu Ibrahim ya shaida wa kotun cewa wani mutum ne mai suna Musa Dahiru ya yi karar abokinsa Karibu […]
Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Shahuci a Kano ta umarci ’yan sanda su tsare wani mutum mai suna Karibu Yahaya bisa zarginsa da sakin matar abokinsa ta waya.
Dan sanda mai gabatar da kara Auwalu Ibrahim ya shaida wa kotun cewa wani mutum ne mai suna Musa Dahiru ya yi karar abokinsa Karibu cewa a ranar 11 ga watan Disamban bara yana Legas matarsa ta kira shi a waya inda ta nemi karin bayani a kan sakon sakin da ya aiko a gaya mata, lamarin da ya sanya shi dawowa gida Kano cikin hanzari.
Malam Musa Dahiru ya kara wa kotu bayani cewa “Bayan ta gaya min abin da ya faru sai na nemi ta ba ni lambar wanda ya kira ta ya gaya mata batun sakin, ina gwada kiran lambar sai sunan Karibu ya bayyana.”
Sai dai wanda ake zargi ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi inda ya ce abokin nasa ya yi haka ne domin ya bata masa suna saboda sun samu matsala a kan kudi. “Kasancewar muna aiki a wata kungiya ta Human Right Watch sai muka yi tunanin bude ofishi a garin Kura sai dai da aka ba mai karar kudin sai ya gaza sauke nauyin da aka dora masa inda ya cinye kudin,” inji shi.
Ya kara da cewa “A wani lokaci na kira wayarsa sai matarsa ta dauka take gaya min cewa ba ya gida amma idan ya dawo za ta sanar da shi. Na yi mamaki lokacin da ya kira ni yake tuhumata da sakin matarsa. Lokacin da na ji wannan magana ni da kaina na kai kara gaban ’yan sandan a garin Kura don sulhuntamu.”
Alkalin Kotun Mai shari’a Malam Hadi Tijjani ya bayar da umarnin ’yan sanda su tsare wanda ake zargi zuwa lokacin da za su gama gudanar da bincike a kan lamarin ta hanyar nemo bayanan gaskiya a kan wayar da matar mutumin ta yi ikrarin Karibun ya yi mata. Ya kuma dage sauraren shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Janairun nan.