Ana zarginta da kashe mijinta ta hanyar kone shi da fetur

Wani magidanci mai suna Abdulhamid Muhammad da ke Unguwar Gayawa a karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano ya rasa ransa sakamakon kone shi da fetur da matarsa Maryam Muhamamd da ba su fi wata biyu da aure ba ta yi. Marigayin ya shaida wa manema labarai kafin ya cika cewa da misalin karfe 11:00 na […]

Ana zarginta da kashe mijinta ta hanyar kone shi da fetur
Ana zarginta da kashe mijinta ta hanyar kone shi da fetur

Wani magidanci mai suna Abdulhamid Muhammad da ke Unguwar Gayawa a karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano ya rasa ransa sakamakon kone shi da fetur da matarsa Maryam Muhamamd da ba su fi wata biyu da aure ba ta yi.

Marigayin ya shaida wa manema labarai kafin ya cika cewa da misalin karfe 11:00 na dare yana kwance sai ya ji an watsa masa wani ruwa-ruwa a jikinsa, kuma kafin ya farga har wuta ta tashi a jikinsa. “Ina kwance barci ya fara daukana sai na ji matata ta watsa min wani abu mai ruwa-ruwa a jikina, kafin in tambaye ta me ta watsa min sai kawai ji na yi wuta ta kama jikina. Kuma kafin a kawo min agaji tuni wutar ta gama lahanta ni,” inji shi.
Marigayin ya ce, a saninsa babu wani abu na sabani tsakaninsa da matarsa da har zai kai ta yi masa wannan aika-aika. “A ranar da abin ya faru da na dawo gida mun zauna da ita mun yi hira sosai. Lokacin da zan fita waje da kanta ta ari wayata don ta yi kallon wani fim din Hausa,” inji shi.
Matarsa Maryam Muhamamd ta ce babu hannunta a kone mijinta, “Ba ni na kona shi ba, ban san yadda aka yi wuta ta tashi a dakin ba, saboda kananzir da ashana suna kicin. Ba mu da fetur a gidan, ni kaina kasancewar ina kwance a kan kujera sai da wutar ta kona ni a hannuwana,” inji ta.
Maryam ta ce babu wani rashin jituwa a tsakaninta da mijinta, ta ce kafin wutar ta tashi sai da suka yi hira. “Abin da zai tabbatar da cewa babu wani sabani a tsakaninmu, a daren da abin ya faru wayarsa ma na ara na yi kallon fim da ita, kasancewar tawa ta baci,” inji ta.
Da aka tunatar da ita cewa mijinta ya ce ita ce ta kona shi, sai Maryam ta ce, “Ban san dalilin da ya sa ya fadi haka ba, amma babu komai, Allah Yana bayan mai gaskiya. Idan ni na kona shi Allah Ya gagauta saka masa, kuma idan sharri ya yi min Allah Ya bi min hakkina duk da cewa ya rasu.”
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya ce rundunarsu na bincike don gano gaskiyar lamarin. “A yanzu haka wacce ake zargin tana hannunmu, duk da cewa ita ma ta samu kuna a hannuwanta. Kwamishinan ’Yan sanda ya bayar da umarnin a mayar da kes din sashin manyan laifuffuka (CID) don ci gaba da bincike. Kuma da zarar mun kammala bincike za mu tura ta kotu don yi mata hukunci,” inji shi.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi