Ana zarginta da yi wa kawarta asiri kan saurayi
Wata budurwa mai suna Habiba Abubakar ta gurfana a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari bisa zarginta da laifin yi wa kawarta asiri a kan saurayi.kawarta mai suna Maryam A. Usman ta shaida wa kotun cewa Habiba Abubakar ta yi mata asiri saboda wani saurayinta lamarin da ya sa Maryam din […]
Wata budurwa mai suna Habiba Abubakar ta gurfana a gaban Kotun Lardi ta
Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari bisa zarginta da laifin yi wa kawarta asiri a kan saurayi.
kawarta mai suna Maryam A. Usman ta shaida wa kotun cewa Habiba Abubakar ta yi mata asiri saboda wani saurayinta lamarin da ya sa Maryam din ta kwanta rashin lafiya.
Maryam ce kawarsu Amina Muhamamd ce ta bayyana mata cewa wacce ake zargin ce da alhakin rashin lafiyarta.
Aminiya ta gano cewa dukkan kawayen uku suna zaune a daki guda a gida mai lamba 17 a Titin Abeokuta a Unguwar Sabon Gari a birnin Kano.
Mai karar ta shaida wa kotu cewa Habiba ta nuna wa Amina wani abu na tsafi da aka lullube shi a cikin gashin tsuntsu tare da bayyana mata cewa wani boka ne ya ba ta don ta yi wa kawarsu Maryam asiri saboda cin amanar da ta yi mata inda ta kwace mata saurayi.
Wacce ake zargin ta amsa laifinta inda ta ce ta yi wa kawarta asirin ne don ramuwar gayya.
Habiba ta kara da cewa ta dauki wannan mataki ne don ta koya wa kawartata hankali bisa kwacen saurayi da ta yi mata.
Alkalin kotun Mai shari’a Faruk Ahmad ya bayar da umarnin tsare wacce ake zargin zuwa lokacin da mai kara za ta samu lafiya, kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 21 ga Afrilu don ci gaba da shari’ar.