Ana zarginta da zubar da cikin tsohon mijinta

Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta kama wata mata mai suna Marakisiyya Muhammad bisa zarginta da zubar da cikin tsohon mijinta ba tare da izininsa ba.Tsohon mijin matar mai suna Surajo Muhamamad ne ya yi karar tsohuwar matar tasa gaban hukumar inda ya ce ya samu labarin tsohuwar matarsa ta daura […]

Ana zarginta da zubar da cikin tsohon mijinta
Ana zarginta da zubar da cikin tsohon mijinta

Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta kama wata mata mai suna Marakisiyya Muhammad bisa zarginta da zubar da cikin tsohon mijinta ba tare da izininsa ba.
Tsohon mijin matar mai suna Surajo Muhamamad ne ya yi karar tsohuwar matar tasa gaban hukumar inda ya ce ya samu labarin tsohuwar matarsa ta daura aure bayan tana dauke da cikinsa da ya dade yana kula da ita a kai. “Tun lokacin da muka rabu da ita ta sanar da ni cewa tana dauke da cikina don haka na ci gaba da daukar nauyin cikin. Duk wata ina kai Naira dubu shida ga Hukumar Hisba a matsayin kudin abincinta har aka yi tsawon wata shida. Kwatsam sai na ji ta daura aure. Babu wata hujja da za ta gaya min in yarda da ita, abin da nake bukata shi ne kawai a fito min da da ko ’yata da aka haifa.”
Sai dai lokacin da Hisba ta tuntubi matar ta ce, “Kimanin wata uku da suka wuce cikin ya zube sakamkon sanar da ita rasuwar kanen mahaifiyarta da aka yi. Lokacin da aka sanar da ni rasuwar kanen mahaifiyata saboda halin da na shiga na rudani sai na yi barin cikin da ke gare ni. Gaskiya na yi laifi a kan rashin sanar da batun zubwewar cikin, ina neman afuwa a kan hakan,” inji ta.
Mataimakin Kwamandan Hukumar na yankin, Malam Abubakar Mati Salihu ya ce matar wurinsu take zuwa take karbar Naira dubu shida a matsayin kudin ciyarwa da tsohon mijinta yake ba ta. “Saboda wannan ha’inci da ta yi Kwamandan Hisba na karamar Hukumar Dala ya yi umarnin a kai ta asibiti sannan idan an karbo sakamakon a hada a gurfanar da ita a gaban kotu,” inji shi.