ANC za ta goyi bayan karbe gonakin Turawa ba tare da diyya ba
Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu, ta ce za ta goyi bayan kudirin da jam’iyyar adawa ta Masu Yakin ’Yancin Tattalin Arziki (EFF) ta gabatar kan karbe gonakin Turawa ba tare da biyan diyya ba. Shugaban Jam’iyyar EFF, Julius Malema ne ya jagoranci muhawara kan wannan batu a majalisar kasar a ranar Talatar […]
Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu, ta ce za ta goyi bayan kudirin da jam’iyyar adawa ta Masu Yakin ’Yancin Tattalin Arziki (EFF) ta gabatar kan karbe gonakin Turawa ba tare da biyan diyya ba.
Shugaban Jam’iyyar EFF, Julius Malema ne ya jagoranci muhawara kan wannan batu a majalisar kasar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya shaida wa ’yan majalisar cewa: “Lokacin sulhuntawa ya wuce. Yanzu lokaci ne na yin adalci. Idan jikokin Jan ban Riebeeck ba su fahimci muna bukatar gonakinmu ba, cewa a kai ne kuma game da martabarmu ce, to sun gaza su karbi kyautar jin kai. Ba ramuwar gayya muke son dauka ba. Amma wajibi ne a karbe wadannan gonaki ba tare da biyan diyya ba domin rarraba su daidai wa daida.”
Minista Ruwa da Kula da Tsabta, Gugile Nkwinti ya ce za su jefa kuri’ar goyon baya ga kudirin.
“Jam’iyyar ANC tana bayar da cikakken goyon baya ga shirin karbe gonakin ba tare da biyan diyya ba kamar da Jam’iyyar EFF ta gabatar,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Ya kamata mu yi watsi da labaran da ake bayarwa cewa an sace gonaki, kamar mutanenmu suna barci lokacin da aka karbe gonakin. An kwace gonakin ne ta hanyar munanan yake-yake na Turawan mulkin mallaka.”
Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta Afirka ta Kudu, Jam’iyyar Democratic Alliance (DA), ta ki amincewa da matsayin jam’iyyun biyu, inda ta yi gargadin cewa “Karbe gonakin ba tare da biyan diyya ba, ba zai kawo maslaha ba.”
Wata kididdigar da sashin kula da kasa ya gudanar a shekarar 2017, ya ce kasha 72 cikin 100 na gonaki da filayen kasar duk mallakar Turawa ne , yayin da sauran fararen fata suka mallaki 15, sai Indiyawa kasha 5, yayin da bakaken fata ke da kasha 4 cikin 100 kacal.
A jawabin da sabon Shugaban Afira ta Kudu Cyril Ramaposa ya gabatar ga jama’ar kasar a makon jiya, ya ce a yayin da yake goyon bayan a karbe gonaki ba tare da biyan diyya ba, ba zai goyi bayan tsarin “kwaci da kanka” ba.