Angela Merkel ta sake samun wa’adin mulki karo na uku

Shugabar Jamus, Angela Merkel ta kara samun wa’adin mulki a karo na uku. ’Yan majalisar ne suka zabeta, ta sake jan ragamar kasar a karo na uku. Wannan mata ’yar shekara 59, ita ce macen farko da ta mulki kasar Jamus, kuma a karkashin jagorancinta tattalin arzikin kasar ya bunkasa fiye da na sauran kasashen […]

Angela Merkel ta sake samun wa’adin mulki karo na uku

Angela Merkel, Germany’s chancellor and Christian Democratic Union leader, left, takes her third term oath beside Norbert Lammert, president of the Bundestag, as the new coalition Government is sworn in at the Reichstag in Berlin, Germany, on Tuesday, Dec. 17, 2013. After cajoling the defeated Social Democratic Party to become her junior coalition partner, Merkel […]

Shugabar kasar Jamus Angelea Merkel ta yi rantsuwar kama aikiShugabar Jamus, Angela Merkel ta kara samun wa’adin mulki a karo na uku. ’Yan majalisar ne suka zabeta, ta sake jan ragamar kasar a karo na uku. Wannan mata ’yar shekara 59, ita ce macen farko da ta mulki kasar Jamus, kuma a karkashin jagorancinta tattalin arzikin kasar ya bunkasa fiye da na sauran kasashen da ke cikin hadakar Tarayyar Turai, masu amfani da kudin Yuro.
Jam’iyyar Angela Merkel ta CDU, wadda take jan ragamar kasar, ta sake samun nasa a zabukan kasar, da aka gudanar cikin watan Satumbar da  ya wuce. Sai dai a majalisar kasar, wadda aka yi wa lakabin Bundestag, rinjayen jam’iyyar ya ragu. Don haka aka yi gwamnatin gamin gambiza da sauran ’yan adawa. Jam’iyyar adawa ta CSD, wadda ta zo na biyu a zaben, ta amince da ci gaban mulkin Angela Merkel, bisa la’akari da tsarin haraji da ta bulllo da shi ban a tursasa wa al’umma ba ne.
Shugabar Jamus na daya daga cikin jiga-jigan shuabannin Turai. Za ta ci gaba da fafutikar yaran tattalin arzikin kasashen da ke fama da matsala a Tarayyar Turai, wadanda da yawansu ke zargin kasar Jamus da haifar musu da matsala. Kuma ministan kudinta na yanzu, Wolfgang Schaeuble zai ci gaba da rike mukaminsa. Jaridar Los Angeles  Times, ta ruwaito cewa, ‘a karkashin Angela Merkel, Jamus na da fada a aji a harkokin siyasar Turai, don ta mamaye ko’ina, musamman in an yi la’akari da karfin tattalin arzikinta.