Ango da amarya
Wani ango ne da amaryarsa da suka yi auren soyayya, suka tare a gidan da mahaifin angon. Da yake suna saman bene ne, shi kuma mahaifin yana kasa, kullum sai su kunna wakar ‘Fifita fita mana shayi, ka sanya mana luna madara.’ Sukan kure karar rediyon, wanda hakan na damun tsohon. Shi kuwa sai ya […]
Wani ango ne da amaryarsa da suka yi auren soyayya, suka tare a gidan da mahaifin angon. Da yake suna saman bene ne, shi kuma mahaifin yana kasa, kullum sai su kunna wakar ‘Fifita fita mana shayi, ka sanya mana luna madara.’ Sukan kure karar rediyon, wanda hakan na damun tsohon. Shi kuwa sai ya rabu da su, bai yi masu magana ba. Ana haka, bayan wasu lokuta kawai sai ya ji suna rigima tsakaninsu. Angon ya biyo ta da gudu da zage-zage. Jin haka sai tsohon ya fito, ya ce: “Kai, har shayin ya huce ne?”
Daga Muhammad Jungudo