Ango da amarya sun sa suturar Naira biliyan 930 lokacin bikinsu

Biki ne na ɗan autan attajirin Asiya, Mukesh Ambani, Anant da amaryarsa Radhika Merchant

Ango da amarya sun sa suturar Naira biliyan 930 lokacin bikinsu

Ɗan attajirin Asiya Ba’indiye Anant da amaryarsa Radhika sun sanya rigunan al’ada guda huɗu da gwalagwalai don bikin aurensu da aka ƙiyasta kuɗinsu sun kai Dalar Amurka miliyan 600 (kimanin Naira biliyan 930) a ranar bikinsu.

An kammala shagulgulan auren mafi tsada a duniya ne, bayan shafe wata biyar ana bukukuwa daga birnin Mumbai zuwa Portofino.

Wataƙila ba a taɓa samun ma’aurata kamar Anant da Radhika suka tara manyan baƙi da suka halarci bikin a jirage daga sassan duniya ba.

Kuma an ƙiyasta kaya da abubuwan da ma’auratan suka sa a jikinsu tun fara shagulgulan bikin sun kai Dala miliyan 600, suturar amaryar ta yi kama da almubazzaranci kamar yadda wasu suke zargi.

Manyan masana a duniya sun haɗu a Indiya don halartar bikin ɗaurin auren ɗan attajirin Asiya Mukesh Ambani.

An shafe watanni ana gudanar da bukukuwa masu ƙayatarwa da ke nuna irin ɗimbin arziki da tasirin da attajirin ke da shi.

Anant Ambani, ya yi alfahari da tarin manyan mutane na duniya da suka halarci bikin.

Manyan mutane da suka halarci bikin sun haɗa da tsofaffin firayi ministocin Birtaniya biyu da manyan ’yan kasuwa da fitattun taurarin fina-finan duniya da mawaƙa daban-daban.

Biki ne na ɗan autan attajirin Asiya, Mukesh Ambani, wato Anant da amaryarsa Radhika Merchant, wanda aka ɗaura aurensu a birnin Mumbai na ƙasar Indiya, bayan shafe watanni ana shagulgulan ango da amaryar waɗanda duka shekarunsu 29.

An gudanar da taron ɗaurin auren a wani katafaren ɗakin taro mai cin mutum 16,000, inda ango da amarya suka zauna aka yi musu ajo a gaban manyan mutane daga sassan duniya.

Gabanin haka an yi wata gagarumar liyafa, inda fitattun mutane a duniya ciki har da tauraron wasan damben nan na duniya John Cena da tsofaffin firayi ministocin Birtaniya Tony Blair da Boris Johnson suka halarta.

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, da fitaccen tauraron fina-finan Indiya, Shah Rukh Khan da Shugaban Kamfanin Samsung, Jay Y Lee na cikin ɗaruruwan mutanen da suka halarci bikin.

Bikin Anant da Radhika da aka faro a watan Disamban bara ya samu baƙi 1,200 da aka gayyata zuwa wata liyafa ta gala da mawaƙiya Rihanna ta baje koli.

Hakan ya biyo bayan wani balaguron shaƙatawa na kwana huɗu a Bahar Rum tare da baƙi 800 a cikin watan Mayu sai wata rawa da mawaƙiya Kate Perry ta yi a filin ƙwallo a Cannes sannan ƙungiyar makaɗa ta Riviera ta Italiya ta biyo baya.

Baƙin sun karɓi rigunan anko masu launi da shigar da ake buƙata mai tambarin lambobin fasahar ƘR da aka riga aka aika a kan wayoyin hannu.

Ayarin likitoci daga sassan duniya ya halarci bikin. Kuma an ɗauki shatar jirage don jigilar mahalarta bikin.

Shugaban Kamfanin Jiragen sama na Club One Air, Rajan Mehra, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, iyalan ma’auratan sun ɗauki shatar jirage domin jigilar baƙin da suka halarci bikin auren da aka gudanar a mako ɗaurin auren.

“Baƙi sun zo daga ko’ina a faɗin duniya, kuma kowane jirgi zai yi jigilar baƙi daga sassan daban-daban na ƙasar nan,” in ji shi.

Mahaifin angon, Mukesh mai shekara 66, shi ne Shugaban Rukunin Kamfanonin Reliance, kamfanin da ya yi zarra a tsakanin takwarorinsa a Indiya.

Mukesh Ambani shi ne kuma mutum na 11 a jerin attajiran duniya, inda ya mallaki kadarorin da suka kai fiye da Dala biliyan 123, kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.

Daga cikin fannonin da kamfaninsa ke zuba jari a ciki har da kashi 40 cikin 100 na kasuwancin waya a Indiya da kuma gasar ƙwallon Kurket ta Indiya.