Ango ya fasa auren amarya ranar biki bayan ya duba wayarta
Wani ango mai suna Joe, ya fasa auren amaryarsa lokacin da suke hanyarsu ta zuwa coci don daurin auren. Angon ya dauki wannan mataki ne bayan ya gano wasu sakonnin a wayar amaryarsa inda ya fusata ya fasa auren, inda amaryar ta yi ta rokonsa ya taimaka ya aure ta. A wani bidiyo da aka […]
Wani ango mai suna Joe, ya fasa auren amaryarsa lokacin da suke hanyarsu ta zuwa coci don daurin auren. Angon ya dauki wannan mataki ne bayan ya gano wasu sakonnin a wayar amaryarsa inda ya fusata ya fasa auren, inda amaryar ta yi ta rokonsa ya taimaka ya aure ta.
A wani bidiyo da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta na Intanet wanda ya janyo muhawara sosai, sakamakon shirin da aka yi ranar bikin. Mutane sun kadu kan cewa lokaci daya an soke biki a kan hanyar zuwa daurin auren wanda aka shirya yi a birnin Abuja. Wadansu mahalarta bikin auren sun yi tunanin ko karancin abincin baki ya sa haka ko kuma wanda ya shirya kayan kade-kade da raye-raye da za a yi ne ya haddasa soke bikin. Wadansu bakin da aka gayyata sun yi ta mamakin yadda manyan baki ke ficewa daga wurin bikin a daidai lokacin da ya kamata a zauna a saurari yadda shagalin zai kasance.
Fasa auren na Joe, ya kasance abin mamaki saboda sanarwar sokewar ta fito ce a daidai lokacin da ma’auratan ke hanyarsu ta zuwa cocin da za a daura auren a Abuja.
A rahoton bidiyon da aka dauka ya nuna cewa, angon ya tsaida motar da aka dauko shi tare da amaryar, inda ya tura mata sakon da ya gani a cikin wayarta sannan ya tabbatar mata da cewa, sakon ya fito ne daga cikin wayarta.
Nan take amaryar ta durkusa a kan gwiwoyinta a gaban angon tana rokonsa cikin jimami, kuma duk da kokarin da ta rika yi don ta kwantar da hankalin angon abin ya ci tura, inda ya fusata yana cewa, sam a bangarensa ya fasa auren. A bidiyon an nuna yadda sauran abokan angon suka yi ta kokarin su roki angon amma ya ki saurarensu, har ta kai ga wani dan uwan amaryar ya je yana rokon angon da kada ya kunyata ’yar uwarsa a cikin jama’ar da suka halarci bikin.
Wadansu sun ce wannan abu da ya faru zai zama darasi ga ma’aurata na su rika tunanin wacce ta dace su aura da shiri na musamman.
Ranar bikin aure tana kasancewa ta musamman da ango da amarya ba za su taba mancewa ba.
Sai dai rana 24 ga Agustan bana da wannan lamari ya faru ta kasance ranar da wadanda aka gayyata suka fita cikin mamaki kan abin da ya faru na fasa wannan daurin aure.