Ango ya rataye kansa wata 4 bayan yin aure a Jigawa

An tsinci gawar angon ce rataye a cikin dakinsa

Ango ya rataye kansa wata 4 bayan yin aure a Jigawa

An tsinci gawar wani sabon ango mai shekara 30, Usman Sani Goga, rataye kansa a Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa.

Marigayin, wanda mai sana’ar daukar hoto ne, rahotanni sun ce ya yi aure wata hudu da suka gabata, an tsinci gawarsa ne a cikin dakinsa da ke unguwar Akula ta garin na Babura.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin hukumar tsaro ta Sibil Difens a Jihar, CSC Adamu Shehu, ya ce ko a ranar da lamarin zai faru, sai da marigayin ya kai matarsa unguwa gidan wasu ’yan uwansa, wajen misalin karfe 2:00 na rana, inda ya yi alkawari zai koma da yamma ya dauke ta.

Sai dai ya ce har yanzu babu cikakken bayani a kan makasudin rasuwar tasa, amma ya ce suna nan suna bincike a kan lamarin.

Da take tsokaci a kan lamarin, matar mamacin ta ce, “Na yi ta kiran wayarsa wajen misalin karfe 5:00 na yamma amma bai daga ba, daga nan ne na yanke shawarar hawa babur din acaba na koma.

“Da na isa gida ne sai na ga ba ni da mabudi, inda na sake kiran wayarsa, amma bai daga ba.

“Sai na samu na shiga gidan da taimakon dan acabar da ya kai ni, inda na ga babur din mijin nawa a ajiye, sabanin yadda na saba gani.

“Ko da na shiga ciki sai na hango shi a rataye a jikin fanka a cikin dakinmu,” in ji matar.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025