Ango ya saki matarsa bayan kwana biyu da aure a Saudiyya
Mutanen Saudiyya da dama sun caccaki wani ango da ya saki matarsa bayan kwana biyu da aurenta, inda ya danganta faduwar labule da da kwalbar turare da yaron gidansa a kanta. Wannan mutum mai camfi ya bayyana cewa, yana zargin akwai wani mummunan abu tattare da amaryarrsa, bayan da ya ga aukuwar wadannan al’amura. Ya […]
Mutanen Saudiyya da dama sun caccaki wani ango da ya saki matarsa bayan kwana biyu da aurenta, inda ya danganta faduwar labule da da kwalbar turare da yaron gidansa a kanta. Wannan mutum mai camfi ya bayyana cewa, yana zargin akwai wani mummunan abu tattare da amaryarrsa, bayan da ya ga aukuwar wadannan al’amura.
Ya ce a ranar zaman aurensu ta farko, labulen dakin da suka zauna don shakatawa ya fado kasa, sannan mai’aikin gidansu ya zame ya fadi a lokacin da ya kawo musu abinci.
Ya kuma ce lokacin da suka dawo gidansu, sai kwalbar turaren da yake rike da ita ta fado kasa, a daidai sa’adda yakle bayyana wa amaryarsa cewa turaren na da kamshi, kamar yadda shafin sadarwar Al Marsad ya ruwaito.
Wannan mutumin dai yana zargin cewa, amaryarsa ce ke tattare da mummunan abin da ya sa wadannana bubuwa suka rika faduwa bayan aurensu. Don gudun mummunan abu ya same shi a rayuwa sai ya yanke hukuncin sakinta.
Washegari kawai sai ya mayar da ita zuwa gidan iyayenta, ya bayyana musu cewa ya saketa.
Jin wannnan al’amari da ya auku tsakanin wannan ango da amaryarsa, sai mutanen da ke ta’ammali da shafukan sadarwa na facebook da twitter a Saudiyya suka rika caccakarsa da sukar lamirin tunaninsa. “Shin yana tunanin cewa, aure karamin al’amari ne,” kamar yadda wani mai shafin sadartwa na blog ya bijiro masa da tambaya.
“”Ko ganin cewa za ka iya auren mace, sannan kasaketa kan kanwkanen al’amari? Wannan mutumin na bukatar taimako. Bai kamata a bar shi ya yi wasa da hankalin mutane ba, saboda bukatun son ransa,” inji shi.
Yara, wata mai mu’amala da kafar sadarwar, yace al’amarin wannan angon wasa ne da shirme damfare a dabi’unsa.
“Dalilan sakin aure na wasa ne, kuma a hakikanin gaskiya al’amarin na nuni da karancin tunaninsa,” kamar yadda ta bayyana.
Shi kuwa wani mai ta’ammali da wannan kafar, taya amaryar ya yi murna da ta rabu da mutumin dabi’arsa ta zama wani bambarakwai. “Ta yi wu ya danganta aukuwar wadannan al’amura ne a kanta,” inji shi. “Wannan mata ta yi matukar sa’a da ta rabu da mutumin da rayuwarsa ke damfare da matsala a tunaninsa,” a cewarsa.
Mai shafin Moniker of Falkon, cewa ya yi, dalilan da mijin ya bayar game das akin auren ba su da ma’ana.
“Wannan ba karamin shirme ba ne, kuma dalili bai yi ma’ana ba,” inji shi. Domin a cewarsa: “Mun san cewa akwai kambun baka (mugun ido), amma mun san akwai addu’o’in da mutane kan yi don neman tsari daga kambun baka (mummunan gani)”