Angola ta kora Namibia gida a Gasar AFCON
Yanzu Angola ta shiga zagayen Quarter-Finals a gasar.
Angola ta kora Namibia gida a Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta AFCON da ke gudana a Ivory Coast bayan da ta doke ta da ci 3-0.
Dan wasan Angola, Gelson Dala ne ya zura kwallaye biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma an dawoAgostinho Mabululu ya zura kwallo ta uku.
- Kungiyoyin Arewa sun soki dauke ofisoshin CBN da FAAN daga Abuja
- Isra’ila ta kashe ƙarin mutum 174 a Gaza bayan hukuncin Kotun Duniya
Wasan ya yi zafin da sai da alkalin wasa ya ba kowane bangaren jan kati – abin da ya sa dukkan su suka karasa wasan da ’yan kwallo goma-goma.
Mabululu ya kafa tarihi a Angola na zama dan wasan kasar na farko da ya taba cin kwallaye uku a gasar kofin nahiyar Afirka.
Yanzu Angola ta shiga zagayen Quarter-Finals a gasar, bayan lallasa Namibia da ta yi a filin wasa na Stade de la Paix
Wannan sakamakon wasa na nufin Angola za ta kara da wanda ya yi nasara a karawa tsakanin Najeriya da Kamaru.
Ana can dai an soma kece-raini tsakanin Najeriya da Kamaru a wasan da Redouane Jiyed na kasar Morocco ka alkalancinsa a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny.